Kiddidiga daga ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin ta nuna cewa, yawan kudin dake shafar cinikin shige da fice kan hidimomi a kasar, ya kai dalar Amurka biliyan 92.7, adadin da ya kai sabon matsayi kuma wanda ke kan matsayin farko a duniya. Yayin baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa wato CIFTIS dake gudana a nan birnin Beijing, abubuwan dake da nasaba da fasahar kirkire-kirkire sun fi jan hankalin kamfanonin ketare mahalarta bikin, kamar makamashi na Hydrogen da batir da fasahar lantaroni da yanar gizo da sauransu. A ganinsu, karkata zuwa sabbin hanyoyin samun ci gaba na da alaka da kowa, suna fatan Sin za ta gaggauta bunkasa cinikayyar hidimomi ta amfani da yanar gizo da na’urori masu kwaikwayon tunanin dan Adam da kiyaye muhalli.
Cikakken zama karo na 3 na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwamins ta Sin karo na 20, ya bayyana cewa, dole ne a nace ga manufar bude kofa da kafa sabon tsarin tattalin arziki mai matukar bude kofa. Kuma gaggauta bunkasuwar cinikayyar hidimomi, muhimmin mataki ne na daga matsayin bude kofa da fitar da sabbin karfin raya cinikayyar shige da fice. Ya zuwa yanzu, Sin ta fitar da matakai fiye da 1,300 na gudanar da aikin gwaji don habaka bude kofa a wannan fanni, a bangarori 13 ciki hadda kimiyya da fasaha da sadarwa da al’adu da yawon bude ido da hada-hadar kudi da sauransu.
Bikin baje kolin CIFTIS a wannan karo ya bayyana kirkire-kirkiren da Sin take yi a bangaren cinikayyar hidimomi, kuma an gano niyyar Sin ta raya sha’anin cinikayyar hidimomi mai inganci, da ma kuzarin aikin zamanintar da al’ummar Sinawa da damammaki da yake samarwa. (Amina Xu)