An yi ta harbe-harben bindiga a Guinea-Bissau a ranar Laraba yayin da shugaban kasar, Umaro Embaló, ya ce an kama shi da misalin karfe 1 na rana a cikin ofishinsa da ke fadar shugaban kasa, yana mai bayyana lamarin a matsayin yunkurin juyin mulki.
Embaló, ya zargi Shugaban Sojojin kasar da jagorantar tawagar sojin da suka tsare shi.
ADVERTISEMENT
Daga cikin wadanda aka tsare, akwai Shugaban rundunar tsaro, Janar Biaguê Na Ntan; Mataimakin Shugaban Sojoji, Janar Mamadou Touré; da Ministan Harkokin Cikin Gida, Botché Candé,.
… cikakken rahoto na zuwa da zarar an samu wani ci gaba














