Wasu majiyoyi a garin Potiskum sun tabbatar da bullar sabuwar cutar nan ta ‘Diphtheria’ a garin, inda a halin yanzu an samu mutuwar yara da dama yayin da aka kwantar da wasu a cibiyoyin kebe majinyata a sibitin garin.
Dr. Umar Chiroma, shi ne mukaddashin babban sakataren hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Yobe, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Lokacin da muka samu rahoton bullar cutar a garin Potiskum a karshen mako, nan take muka hada tawaga zuwa wuraren da abin ya shafa don wayar da kan jama’a tare da dakile yaduwarta cikin al’umma, ”
- Yanzu-yanzu: Hon. Buba Mashio Ya Zama Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Yara 2 Da Mahaifinsu Kan Kashe Wani Mutum A Yobe
“Duk da a yanzu ba za mu iya bayyana shi a matsayin Diphtheria ba har sai mun dauki samfurin kwayar cutar mun bincika daga nan za mu iya sanar da abin da ake ciki.”
‘’Wasu daga cikin majinyatan sun haura shekaru 30, wasu 14 yayin da wasu kuma ‘yan shekara 12 zuwa 8 ne. Sannan wani abin takaici shi ne, wasu daga cikin majinyata suna daga cikin wadanda suka bijirewa allurar riga-kafi, wanda hakan ya sa ya fi shafar yaran da ba su yi riga-kafin ba.” In ji shi.
Dr. Chiroma ya kara da cewa, ‘’Wasu daga cikin majinyatan sun warke, don haka ba za mu iya tabbatar da cewa cutar Diphtheria ce har sai idan binciken masana ya gano ita ce, ”
“Da safiyar yau Talata na samu labarin bullar cutar daga daraktan da yake kula da wannan shiyya, saboda haka har yanzu ba mu sami adadin mace-macen a hukumance ba.” Cewar Dr. Chiroma.
Unguwanin da abin ya fi kamari sun hada da unguwar Tandari, Misau Road, Sabuwar Sakateriya, Arikime, Ramin Kasa, Boriya, Yuganda da Texaco quarters.
Wata majiya daga cibiyar kebance majinyata na asibitin kwararru da ke Potiskum ta bayyana cewa suna fuskantar karancin magungunan da za su shawo kan lamarin.
Wata majiya ta shaidawa wakilinmu cewa sama da mutum 46 ne aka kwantar a asibitin, inda yara 20 suka mutu a gida tare da karin wasu 4 da suka mutu a asibitin.
Abdullahi Muhammad, daga garin na Potiskum ya ce ‘’Yara da dama sun mutu a gida kafin a kai su asibiti, wannan cuta ce mai saurin kisa.”
‘’Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakin ceto rayukan jama’a, daga wannan cuta wadda mun lura ta na dauke da zazzabi, tari, kashe jiki da sauransu.”
A nashi bangaren, jami’in kula da riga-kafi na karamar Hukumar Potiskum, Mallam Buba, ya musanta alkaluman wadanda suka mutu ta sanadin cutar, amma ya ce a kalla yara 42 ne ke kwance a asibiti.