Kwamishinan yaɗa Labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya nemi a yi kiranye ga Hon. Ali Sani Madakin Gini daga Majalisar Tarayya, yana zarginsa da rashin yin wakilcin da ya dace ga al’ummar mazabar Dala ta Jihar Kano a Majalisar Wakilai.
Waiya ya bayyana wannan bukatar ne a taron haɗin gwuiwar masu ruwa da tsaki da reshen Jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Dala.
- ‘Yansanda Sun Cafke Ali Madakin Gini, Kan Zargin Amfani Da Bindiga A Yakin Zaben NNPP Na Kano
- Rikicin Jam’iyyar NNPP Ya Kazanta A Kano
Ya nuna rashin jin daɗinsa game da wakilcin Madakin Gini, inda ya ce rashin bin ƙa’idojin mazabarsa na bukatar a sauke shi daga Majalisar. “Mutanen ƙaramar hukumar Dala sun cancanci samun wakilci mafi kyau. Kiranye ga Hon. Madakin Gini daga Majalisar tarayya yana da muhimmanci don warware buƙatu da damuwar al’ummarmu,” in ji Waiya.
Kwamishinan ya jaddada muhimmancin siyasar ƙaramar hukumar Dala, yana mai cewa tana ɗauke da yawan kwamishinoni a cikin majalisar zartarwar jihar Kano da shugaban majalisar dokokin jihar.
A baya LEADERSHIP ta bayyana cewa Madakin Gini ya bayyana a bainar jama’a cewa ya bar tsarin Kwankwasiyya a bara, amma bai ajiye mukamin da ya samu a NNPP ba.
Kwamishinan ya yi ikirarin cewa ayyukan Madakin Gini na nuna rashin jajircewa ga waɗanda suka zaɓe shi. “Madakin Gini ya bayyana cewa ba ya cikin waɗanda suka goyi bayan shi da suka zabe shi. Saboda haka, babu dalilin ci gaba da kasancewarsa a wannan muƙamin idan ba ya wakiltar buƙatun mutanen Dala.
Da zarar shugabannin jam’iyyar sun amince, ni na shirya fara aiwatar da aikin kiranyesa,” in ji Waiya. Taron ya samu halartar shahararrun mutane, ciki har da Alhaji Lawan Husaini Dala, shugaban NNPP na Dala; da Alhaji Dayyab Ahmad Maiturare, Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, da Hon. Suraj Kwankwaso, da sauransu.