Gwaman Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce akwai wasu masu fada a ji a fadar Aso Rock da ke yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, zagon kasa don faduwa zabe mai zuwa.
Ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Arise da safiyar ranar Laraba.
- An Hallaka Matashi 1, An Jikkata Wani A Yakin Zaben APC A Bauchi
- Gwamna Inuwa Ya Amince Da Biyan Giratuti Na Naira Biliyan 1.3 Ga Ma’aikatan Kananan Hukumomi
El-Rufai bai bayyana sunayen mutanen ba, amma ya ce suna cike da takaicin yadda Tinubu ya doke ‘yan takararsu a zaben fid-da-gwanin shugaban kasa da APC ta gudanar, abin da ya sa suka shiga shirya makarkashiya domin ya fadi zabe.
El-Rufai, ya ce mutanen na fakewa ne da muradin shugaba Buhari na yin abin da yake ganin ya dace.
“Suna kokarin ganin lallai sai mun fadi zabe, kuma suna fakewa da burin shugaban kasa na yin abin da yake ganin ya dace.
“Zan ba da misali guda biyu: wannan tallafin man fetur da ake kashewa na tiriliyoyin Naira, tuni muka amince a janye”.
Kazalika, El-Rufai ya ce ya yi wata tattaunawa da Buhari a 2021, inda ya nuna masa illar da ke cikin ware sama da tiriliyan biyu wajen biyan tallafin man fetur bayan ana kashe Naira biliyan 200 kacal a kasafin kudin gudanar da manyan ayyuka.
Ya ce shugaban kansa ya gamsu, hakan kowa da ke cikin gwamnati ya amince da batun cire tallalfin na man fetur.
Dangane da batun sauya fasalin takardun kudin Naira da kuma takaita cire kudi, Tinubu ya yi zargin ana shirya masa bita da kulli ne don ganin ya fadi zabe.
Sai dai kuma daga bisani ya bayyana cewar ba a fahimci maganarsa ba ne, amma ha ce yana da cikakken goyon bayan shugaba Buhari.