Jami’an hukumar tsaro ta Jihar Ondo da aka fi sani da Amotekun an yi zargin azabtar da wani yaro dan shekara 14 mai suna Ayomide Adeghalu har lahira.
Lamarin ya faru ne a garin Ondo da ke karamar hukumar Ondo ta Yamma.
- Ba Mu Amince Da Yin Zanga-Zanga Kan Tsare Malaminmu Ba – Daliban Dakta Idris Dutsen Tanshi
- Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Lasisin Bude Jami’ar Koyo Daga Gida Da Karin Wasu 37
Leadership Hausa ta tattaro cewa Ayomide, wanda ke zaune tare da matar mahaifinsa a unguwar Ogbonkowo da ke Odojomu a cikin garin Ondo, kan taban N500 da aka aike shi.
Sai dai an ce matar mahaifinsa ta fusata ne saboda gazawar yaron ya yi bayanin yadda kudin suka bace kuma ta yanke shawarar hukunta shi domin ya bayyana gaskiya.
Wata majiya da ta zanta da wakilinmu da ya nemi a sakaya sunanta, ta ce bayan an yi masa hukunci mai tsanani, an mika yaron ga jami’an Amotekun wadanda suka azabtar da shi don tilasta masa ya bayyana gaskiyar lamarin.
“Yaron matashin ya fuskanci hukuncin da ya dauki tsawon sa’o’i da dama, duk da rokon da matar mahaifinsa ta yi na a saki yaron.
“Daga baya, matar ta mika shi ga jami’an Amotekun, inda aka gana masa azaba. Ya samu rauni sosai. Har zuwa lokacin da aka garzaya da shi asibitin kwararru da ke Ondo, likitocin da ke bakin aiki sun tabbatar da rasuwarsa,” in ji majiyar.
An tattaro cewa daga baya an kai rahoton lamarin a ofishin ‘yansanda na Fagun da ke Ondo, yayin da aka ajiye gawar yaron a dakin ajiyar gawa.
Da take nuna alhinin rasuwar dan nata, mahaifiyar marigayin, Maryamu, ta ce ta rabu mahaifinsa ne shekaru kadan da suka gabata.
Ta bayyana cewa, makwabta ne suka sanar da ita halin rashin lafiyar yaron.
“Na yi mamakin mutuwar Ayomide saboda ya kasance mai hazaka kuma abun kaunata.
“Bai taba korafin wata cuta gare ni ba. Abin bakin ciki ne a gare ni na samu labarin cewa wasu jami’an tsaro sun azabtar da shi wanda ya yi sanadin mutuwarsa har lahira saboda bacewar Naira 500,” in ji ta.
Kokarin da Leadership ta yi don jin ta bakin Mista Adetunji Adeleye, Kwamandan Rundunar Amotekun ya ci tura.
Sai dai wani jami’in hukumar tsaron yankin ya shaida wa wakilinmu cewa tuni aka fara bincike a kan lamarin.