Ana zargin wani daga cikin hadiman ‘yar majalisar dokokin Jihar Kaduna da ke wakiltar mazabar Lere ta gabas, a kan yin Luwadi da wani Almajiri dan shekara 13.
Isah wanda ke da zama a Angwar Mangu Sabon Layi a Garin Saminaka da ke a Karamar Hukumar of Lere, an ruwaito cewar, ya jima yana yi wa Almaijrin wanda aka sakaya sunansa, fyaden tare da kuma gargadin yaron kar ya kuskura ya gaya wa kowa aika-aikar.
- Zanga-zangar Karin Kudin Wuta: Gwamnati Ta Shelanta Matakin Da Za Ta Dauka
- Yadda Sin Da Rasha Suke Mu’amala Da Juna Ya Samar Da Kwanciyar Hankali A Duniya
Sanadiyar wannan aika-aikar da aka yiwa yaron, ta janyo an dai kwantar da shi a asibtin kwarru na Barau Dikko da ke Kaduna saboda rashin lafiyar da ya kamu da ita sakamakon badalar da wanda ake zargin ya yi masa.
Yaron a hirar da aka yi dashi a asibitin ya ce, hadimin ya jima yana yi masa luwadi, inda ya ce, sanadiyar badalar ce, ya kamu da rashin lafiya
Malamin makarantar yaron wanda kuma kawun yaron ne mai suna Zayyanu Haruna ya bayyana cewa, yaron na matukar jin jiki sakamakon aikata masa ta’asar.
Shi kuwa jagoran makarantun Tsangaya na kasa Mallam Bala ya ce, sun shafe kwanuka tara a asibitin ana duba lafiyar yaron ba tare da ‘yansanda sun kawo wani rahoto a hukumance kan aukuwar lamarin ba.
An nemi jin ta bakin shugaban asibitin na Barau Dikko kan lamari Farfesa Abdulkadir Musa Tabari amma bai ce uffan kan batun ba.
Wasu rahotanni sun ce, wasu jami’an gwamnatin jihar, na kokarin sakaya maganar.