Umar A Hunkuyi" />

Annobar Korona Na Sake Yaduwa A Nijeriya

Ya zuwa misalin karfe 11:15 na safiyar ranar 31 ga watan Maris, hukumar hana yaduwar cutuka ta kasa (NCDC), ta tabbatar da yawan mutanan da suka kamu da annobar nan ta Koronabairus a cikin kasar nan ya zuwa mutane 135, inda kuma hukumar ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a sakamakon kamuwa da cutar.

An kuma bayar da rahoton bullar cutar a Jihohin kasar nan guda 11 gami da babban birnin tarayya Abuja.

Jihar Legos ce ke kan gaba wajen yawan wadanda suka kamu da cutar ta Koronabairus a kasar nan, inda mutane 81 cikin 135 da aka tabbatar da kamuwarsu duk daga Jihar ta Legos ce suka fito, mai biye mata ita ce babban birnin tarayya Abuja da mutane 25 wadanda suka kamu da cutar ta Koronabairus.

Sai Jihar Oyo mai biye masu da mutane 8 da suka hada har da Gwamnan Jihar, Seyi Makinde, wanda gwajin ya tabbatar da kamuwarsa da cutar ta Koronabairus a ranar Litinin.

In an hada da sabbin mutane hudu da aka shelanta kamuwarsu da cutar a ranar Talata, Jihar Osun ta yi tsalle daga matakin mutum guda da ya kamu da cutar inda a yanzun ta haura zuwa mutane Biyar da aka tabbatar da sun kamu da cutar ta Koronabairus.

A yanzun haka kuma Jihar Kaduna tana da mutane Biyar da aka tabbatar da sun kamu da cutar ta Koronabairus da suka hada da Gwamna Nasir El-Rufai.

Jihohin Edo da Bauci kowaccensu tana da mutane biyu da aka tabbatar da kamuwarsu da cutar ta Koronabairus, da suka hada da Gwamna Bala Mohammed, inda a Jihohin Ekiti, Ribas da Benuwe kowacce ke da mutum guda-guda mai dauke da cutar ta Korona.

A wani labarin kuwa, an tabbatar da samuwar karin mutane udu da suka kamu da cutar Koronabairus a kasar nan.

A cewar cibiyar hana yaduwar cutuka ta kasa (NCDC), an sake samun mutane Uku ne a Jihar Osun da kuma wani mutum guda a Jihar Ogun.

Ya zuwa yanzun dai hukumar ta NCDC ta tabbatar da kamuwar jimillan mutane 135 da annobar ta Koronabairus a cikin kasar nan, inda kuma ta tabbatar da mutuwar mutane biyu cikin wadanda suka kamu da cutar ta Koronabairus.

 

Exit mobile version