Khalid Idris Doya" />

APC A Bauchi Ta Gargadi Yakubu Dogara Kan Yunkurin Tsige Buhari

A karshen makon jiya ne jagororin jam’iyyar APC a kananan hukumomin Dass, Tafawa Balewa da kuma Bogoro suka yi wani ganganko zuwa sakatafiyar jam’iyyar APC da ke Bauchi domin kai korafinsu akan Kakakin Malajisar Tarayya Honorabul Yakubu Dogara a bisa abun da suka kira da kokarinsa na sanya hanu domin tsige shugaban kasa Buhari.

Jagororin APC din, wadanda suka yi umumu suka suka taso daga kananan hukumomin wadanda wannan yankin ita ce mazabar da shi Yakubu Dogaran ke wakiltar a majalisar wakilai ta kasa, sun nuna damuwarsu gaya kan yadda suka riski lamarin, suna masu gargadin Dogara da ya tsame hanunsa ko kuma su yi masa kiranye ko kuma tsigeshi.

Bayan shaida korafinsu a baki, jagororin APC a kananan hukumomi ukun, sun kuma gabatar da korafinsu a rubuce hade da mikata ga uwar jam’iyya domin ita ma ta yi nata kokarin don amsa musu kokensu, takardar mai dauke da sanya hanun dukkanin jagororin APC su 81 a kananan hukumomin sun nuna rashin amincewarsu kan yunkurin Dogara.

Da yake jawabi a wajen kai korafin, shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Bogoro Malam Haruna Rikaya ya ce yaka yi; “Abun da ya kawo mu nan, mu jagororin APC na Bogoro mu 27 mun zo ne domin mu ja kunnen wa shi Speaker Barista Dogara Yakubu game da abun da ke faruwa a can Majalisar kasa. Mun samu labarin sun yi wani tattaunawa na hadin guiwa a tsakanin Dattawa da na Wakilai, inda suke tattauna yadda za su tube shugaban kasa, Muhammad Buhari.

“Wannan shi ne abun da ya sa muka zo domin mu shaida muku cewar mu a jagororin APC a Bogoro ba mu tare da wannan yunkurin nasu, kuma bada yawunmu Dogara ya tsunduma kansa cikin wannan lamarin ba. don kuma muna gargadin Dogara da cewar wannan lamarin bai dace da shi ba,” In ji Rikaya.

Shi kuma Zubairu Musa Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Dass cewa yake yi “Mun zo nan ne domin mu nuna rashin jin dadinmu a game da abun da danmu da muka zaba a mazabar Dass, Tafawa Balewa da Bogoro, to gaskiya mun yi bakin ciki kwarai a bisa yadda ya tsoma kansa cikin wata hidima, kuma ba za mu lamunta ba.

“Kokarinsu na tsige shugaban kasa ba za mu lamunta ba; domin mu APC muna masu yi masa biyayya, ba kuma za mu zura ido suna irin wannan abun ba. a yanzu muna jan hankalinsa ya yi karatun ta nutsu, in ya ki za mu dau mataki na gaba,” In ji shugaban APC.

Shi ma dai shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Tafawa Balewa wanda mataimakinsa Wakili Ahmadi ya wakilta a yayin isar da takardar koken wa uwar jam’iyya, ya yi karin haske kan makasudin zuwansu, yana mai bayanin cewar dukkanin jagororin APC su 27 a karamar hukumar ne suka yi zama domin fitar da matsayar yi wa Dogara gargadi da jan kunne; “Mun tura su Dogara amma abun takaici abun da muka turasu basu suka je suke mana ba; sun je su yi fada da wannan su yi da wancan, a lokacin da aka zo yi zaben jam’iyya sun ki shiga cikin jam’iyya a sakamakon rashin biyyarsu. Amma yanzu abun da Dogara ke kokarin jefa kansa ba za mu lamunta ba,” In ji Wakili.

“Sun hada kai da shi da shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki suna neman cire Buhari ba za mu amince da wannan ba,” A cewar shi.

Ita kuma shugaban mata na jam’iyyar APC a Dass, Rukayya Salihu ta ce; “Gaskiya muna godiya da irin hakurin da Buhari ya yi ta yi da wadannan ‘yan talikan, amma yanzu mu mata mun ce ba mu yarda ba za mu kawo karshen wannan matsalar. Cin mutuncin da Dogara ya ke yi wa Buhari ya isa haka,” In ji Rukayya.

Har-ila-yau shugaban mata na Bogoro Mery Jone cewar take; “Muna magana ne a kan yunkurin Sanatoci da Wakilai da suke yunkurin tsige Buhari, muna masu shaida musu cewar su janye hannayensu daga maganar cire Buhari. Dogara shi ne ya nuna mana Buhari muka yi shi, shi ya nuna mana M.A Muka zabeshi a matsayin gwamna, amma yau a zo a ce mana basu shiri ba mu son hakan, su shirya kansu domin mu tafi tare a APC,” A ta bakinta.

Maryamu Habila shugaban mata na APC reshen Tafawa Balewa ta ce “Don Allah Dogara ka ji tsoron abun da ya wakana a kwanakin baya muka kau da kai. karatu ya baka azancin rike aiki ba wai ya dagular da kai ba ne. taka mu da kuka yi ta yi mun hakura, amma fa babban nan da kuke cakala muna shaida muku ku ji tsoron yin hakan, ku kuma ji tsoron dan adam, kada ka kuskura mu hada ka da Allah ka samu la’ana,” In ji ta.

Da yake amsar wasikar da jagororin APC a kananan hukumomi ukun suka sanya wa hanu, wadanda yawansu ya kai 81 daga Tafawa Balewa, Dass, da kuma Bogoro shugaban jam’iyyar APC a jihar Bauchi Alhaji Uba Ahmad Nana ya gode wa daukan mataki na hankali da jagororin APC suka yi wajen bayyana korafinsu, ya shaida cewar uwar jam’iyya za ta duba korafinsu hanu biyu-biyu domin yin abun da ya dace da ita a matsayinta na uwa.

Uba Nana wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Muhammad A. Hassan ya shaida cewar a matsayinsu na uwa ga duk dan APC za su fada wa ‘ya’yanzu domin saitasu, “Abun da ya kamata ku ku yi, kun yi, kuma ku ci gaba da yin hakan duk abun da ya faru ku kuke kai kara gaba domin daukan matakin da ya dace.

“Game da wannan abun da ke faruwa mun ji kuma bamu ji dadi ba; amma cikin yardar Allah a zatonmu kan wannan matsalar an zo karshe domin shi wanda kuke magana a kansa muna kyautata zaton dane mai jin magana wannan ya zama na karshe ba sai sa baki ba, ko kuma idan yana ganin ana yi zai hana,” In ji Shugaban.

Jam’iyyar ta kara da cewa sai dai uba kan haifi da amma dan ya kasance bai jin maganar uban nasa, don haka ne ya yi fatan dansu ba zau kauce wa wannan ba.

Shugaban APC ya yi fatan sauyawa daga wanda aka gabatar da korafin a kansa.

 

Exit mobile version