Daga, Sharfaddeen Sidi Umar,
Jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato a jiya ta kaddamar da sababbin shugabannin rikon kwarya a matakin Jiha da Kananan Hukumomi 23.
A jawabinsa a wajen taron, jagoran jam’iyyar a Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana cewar sake nada su a matakin rikon kwarya da aka yi ya biyo bayan nasarorin da suka samu a shugabancin su.
Sanata Wamakko wanda ke wakiltar Sakkwato ta Arewa a Majalisar Dattawa ya bayyyana cewar al’ummar Nijeriya na sane da goyon bayan APC da jama’ar Sakkwato ke yi yana cewar za su ci-gaba da jajircewa domin ganin jam’iyyar ta kara karfi a dukkanin matakai.
Ya ce, da ba don Wamakko, goyon bayansa da karfafa guiwarsa ba da ba su samu nasarorin da suka samu ba haka ma ya ce APC ce jam’iyyar da ‘yan Nijeriya suka yadda tare da amanna a kodayaushe.
Shugaban Riko na Jam’iyyar, Isa Achida ya bayyana cewar jam’iyyar ta jefa kuri’ar amincewa da mulkin Muhammadu Buhari a kokarinsa na kyautata rayuwar al’umma. Ya ce duk da kalubalen da kasar ke fuskanta, Buhari ya samu nasarar aiwatar da ayyuka da dama a fadin kasar.