Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, muna muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya. Mafi munin ta’addanci da cin mutunci shi ne, wanda dan ta’adda zai yi a kan al’umman Musulmai kuma ya fito a gaban duniya yana karanta ayoyin Al-kur’ani wadanda Musulmai suka yi imani da shi, yana nuna cewa addini yake yi wa aiki.
Kamar wannan bai isa ba, har kuma da cewa Musulmai wadanda suke kashewa su tuba.
Wannan ta’addanci na Boko Haram ba kawai ya sabawa karantarwa Musulunci ba ne, ya ma fita daga abun da hankali zai dauka. Suna bayyana tabuwar kwakwalwarsu a fili a duk lokacin da suka aiwatar da ta’addanci a doron kasa kuma suka ambaci sunan Allah SWT wanda ya yi umurni da a zauna lafiya, kuma ya yi tanadin mafi munin makoma ga mai kashe muminai.
‘Yan ta’addan Boko Haram suna samun daman hallaka al’umma ne sakamakon munin yanayin tsaro da muke da shi a Nijeriya. In ba haka ba, a ina ne za a bi mutane a dinga musu yankan rago a gonakinsu, alhalin akwai gwamnati kuma akwai jami’an tsaro wadanda a kullum hakkin kare rayuka da dukiyoyi, Allah ya daura musu.
Manoman da aka yi wa yankan rago ba kowa ba ne, ba jami’an gwamnati ba ne, ba jami’an tsaro, ba ma’aikatan kamfani ba ne, su dai sun kasance manoma masu shuka abun da za su ci kuma su yi ta aiki akai har amfani ya fito su kai gida. Irin wadannan mutane ba su damu da komai ba, ba su damu da kowa ba, ba su ce gwamnati ta ba su aiki ba, ba su ce gwamnati ta noma musu tuwo ba, su dai sunce za su noma kuma za su ci. Irin wadannan mutane ne fa aka kashe.
Masu zuciyar fita su noma wa iyalansu suna da yawa a Nijeriya. Amman yanzu suna cikin mawuyacin hali irin wanda ba su taba gani ba. A Jihar Borno ana bin su a yanka su yankan rago. A Jihar Katsina ana dauke su a yi garkuwa da su, a Jihar Zamfara ‘yan ta’adda suna bin su har gonakinsu suna sanya musu haraji mafi karanci N500, 000.
Hanyoyinmu a Arewa sun zama tarkon ‘yan fashi da masu bindiga dadi da masu garkuwa da mutane da jami’an tsaro masu karban na goro. Idan ka koma gidajenmu kuwa, nan ma ba mu tsira ba. A cikin kankanin lokaci a Arewacin Nijeriya harkar satan mutane ya girma ya yi muni. Na tabbatar kuna da masaniya a kan cewa yanzu birni da kauyuka ana dauke mutane ana karban kudade.
Mun gani da idanun mu inda Boko Haram suka kama sojoji suka musu yankan rago, mun ga inda suka kama dan sanda suka fasa mai kai da harsashi, mun ga inda Boko Haram suka kama malaman addini, mun ga inda suka kai wa gwamna da kansa hari, mun ga inda suka tayar da boma-bomai a cikin al’umma suna sallah.
Masu garkuwa da mutane kuwa suna kamawa. Sun kama mahaddacin Al-kur’ani sun ce a ba su miliyan dari uku, sun kama malamai, sun kama jami’an tsaro sun karbi kudin fansa. Sun kama talaka sun karba, sun kama mai kudi sun karba. Sun kama surukin dogarin shugaba Buhari.
Zan iya yin hasashe cewa ko shugaban kasa wanda shi ne aka fi bai wa tsaro a kasar shi ma baya cikin aminci. Jiharsa ta zama filin wasan ‘yan sace mutane da ‘yan bindiga dadi. Yankinsa na Arewa kullum binne gawaki ake yi. Ana binne tsoffi da mata da kanan yara da masu kudi da talaka da marasa galihu.
Jinin wadanda ake kashewa alhaki ne. Kuma zai rataya a kan duk wanda ya kashe da wanda yake karban albashi a kowani wata a kan yana shugabantan al’umma, wacce shugabancin ta ya hada da kare rayuka da dukiyoyi. Matukar mutum yana rikke da mukami kuma yana karban albashi, musamman shugaban kasa wanda shi ne “Commander In Chief” na rundunar tsaron Nijeriya.
‘Yan ta’adda musamman wandanda suke garkuwa da mutane suna dogara ne da wasu miyagun mutane a cikin mu. Kai ba ma su kadai ba, ba a taba cin gari da yaki sai da ‘yan garin. Mataki na farko wurin dakile fitinan ta’addanci a Nijeriya shi ne, al’umma kar su yadda su bar wani baragurbi a cikin su ba tare da sun ankarar da hukuma ba kuma su yi tarayya da ‘yan sanda wajen yaki da ‘yan ta’adda.
Dole gwamnati ta dauki mataki a kan halin da ake ciki. Duk wani mataki da zai tsayar da zubar da jinanenmu dole ne gwamnati ta dauka ko da kuwa hakan zai saba da matsalar kowani mahaluki. Jinin da aka zubar kuma alhaki ne da ba zai taba faduwa kasa banza ba.
Allah SWT ya ba mu zaman lafiya mai dorewa.
Sako daga Mahmud Isa, Yola.
08106792663
“Godiya Ta Samman Ga dan Madamin Daura”
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. Hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jini baki daya. Edita dan Allah ina so ka bani dama domin in yi godiya ga dan Madamin Daura, Hon Musa Haro Daura a kan irin taimakon da yake yi wa masu karamin karfi a cikin alamurran yau da kullum masamman a bangaren ilimi da lafiya.
Hakika Musa Haro yana yin iyakar bakin kokarinshi a kan taimakon jama a duk da cewa baya da wani mukami a gwamnatance, amma duk da haka a yanzu dai ‘yan siyasar yankin Daura babu wanda yake taimakon jama’a kamar Musa Haro. Dan haka babu abin da zamuce da Musa Haro sai dai muce Allah ya saka masa da alkairi. Allah ya biya shi, amin.
Sako daga hadi tsohon sarki Daura
08164205067