Wasan da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta doke abokiyar karawarta West Ham United a filin wasa na London Stadium ya kafa tarihi a matsayin wasa na hudu a tarihin gasar Firimiya da aka jefa kwallaye 7 a mintuna 45 na farko.
Tun a minti na 10 da fara wasan dan wasan bayan Arsenal Gabriel Magallhaes ya jefa kwallo a ragar West Ham, Trossard, Odegaard, Harvertz da Saka ne suka zurawa Arsenal sauran kwallayenta 4 a wasan na jiya Asabar.
Itama West Ham ta fara zura kwallo ta hannun Aron Wan Bissaka kafin Emerson ya zura wata kayatattar kwallo a bugun tazara,jimillar kwallaye 7 da kungiyoyin su ka zura a mintuna 45 na farko ya sa wannan wasa ya zama na hudu da aka taba irin haka a tarihin gasar Firimiya ta kasar Ingila.
Sauran wasannin da aka zura kwallaye 7 a mintuna 45 na farko a tarihin gasar Firimiya sune:
- Blackburn Rovers 3-4 Leeds (14 Satumba 1996).
- Bradfort City 4-3 Derby County (21 Afrilu 2000).
- Reading 3-4 Manchester United (1 Disamba 2012).
- West Ham 2-5 Arsenal (30 Nuwamba 2024).