Connect with us

WASANNI

Arsenal Ta Dakatar Da Tattaunawa Da Ramsey A Kan Sabon Kwantaragi

Published

on

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa, kungiyar Arsenal ta dakatar da tataunawar da take yi da dan wasanta Aaron Ramsey akan sabon kwantaragi, saboda tattaunawar ba ta tafiya yadda ya kamata.

Arsenal da dan wasan dai sun dauki tsawon watanni suna tattaunawa akan sabuwar yarjejeniyar da kungiyar take son sake ba wa dan wasan, sai dai kawo yanzu an dakatar da tattaunawar  duk da cewa saura watanni kwantaragin dan wasan ya kare.

Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa, Ramsey bai gamsu da tayin albashin da kungiyar ta yi masa ba idan har ya kara sabon kwantaragi, yayin da shi kuma yake son karin albashi mai yawa hakan ya sa tattaunawar ta su take samun tangarda.

Idan har ba su cimma yarjejeniya a tsakaninsu ba, dan wasan zai iya barin kungiyar a karshen kakar wannan shekarar ko kuma kungiyar ta sayar da shi a watan Janairu da araha, saboda saura watanni shida yarjejeniyar ta kare daga watan Janairu. An bayyana cewa a farkon wannan kakar kungiyar ta Arsenal ta yi fatali da tayin kudi kusan fam miliyan 50 daga wata kungiya da ba’a bayyana sunanta ba domin sayan Ramsey, sai dai kawo yanzu babu kungiyar da za ta sake taya shi da wannan kudin.

Kungiyoyin Chelsea, da Liberpool da Lazio da Manchester United ne dai suke bibiyar dan wasan kuma ba za su taya dan wasan fam miliyan 50 ba a yanzu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: