A shirye-shiryen da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ke yi na tunkarar sabuwar kakar wasan ƙwallon ƙafa da za a fara a watan Agusta.
Arsenal din ta kammala ɗaukar Riccardo Calafiori daga Bologna a kan zunzurutun kuɗi har Yuro miliyan 43, ɗan wasan bayan mai shekaru 22 ya rattaɓa hannu inda zai shafe shekaru 5 a Emirates Stadium.
Manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da suka haɗa da Real Madrid da Juventus sun nemi ɗan wasan na ƙasar Italiya amma dai ya zabi ya koma Arsenal bayan tattaunawa da makusanta da kuma Mikel Arteta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp