Juma’ar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na nuna alamar kyau duba da yadda Larabar ta ta ke a halin yanzu, Arsenal dai ta kasa lashe kofin gasar Firimiya shekaru biyu a jere inda Manchester City ke lashewa.
Amma a wannan karon iyalan na Wenger kamar yadda ake masu kirari na kokarin ganin sun lashe kofin Firimiya domin zuwa filin wasa na Emirates Stadium su nunawa magoya baya bayan shafe shekaru 21 tun Firimiya ta karshe da suka lashe a shekarar 2004.
- Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 7 Cikin Jerin Sassan Da Ba Za A Iya Dogaro Da Su Ba
- An Samu Adadin Shige Da Fice Miliyan 610 a Kasar Sin
Doke Tottenham da ci 2-1 a daren yau Laraba ya rage tazarar maki dake tsakaninsu da Liverpool wadda ke jan ragamar teburin gasar Firimiya Lig ta kasar Ingila.
Rashin Saka bai hana kungiyar dake birnin Landan zurawa abokiyar karawarta Tottenham Hotspur kwallaye biyu a cikin mintuna biyu ba a wasan na mako na 21 da suka buga.