Abba Ibrahim Wada" />

Arsenal Za Ta Sayi ’Yan Wasa Biyu Daga Sampdoria

Kungiyar  kwallon  kafa ta Arsenal tana zawarcin ‘yan wasan  kungiyar  kwallon  kafa ta Sampdoria guda biyu Dennis Praet da kuma dan wasa Joachim Andersen a  ko karin da kociyan  kungiyar yakeyi na gyara  kungiyar a kakar wasa mai zuwa.

Kociyan  kungiyar, Unai Emery dai yayi al kawarin zai gyara  kungiyar ta hanyar siyan sababbin ‘yan wasan da zasu taimkawa  kungiyar bayan da takasa lashe kofin Europa da tayi rashin nasara a hannun Chelsea sannan kuma basu samu tikitin kofin zakarun turai ba.

Shugabannin  kungiyar dai sunyi al kawarin ba za su bawa Emery ma kudan kudade ba domin siyan ‘yan wasa inda wasu rahotanni suka bayyana cewa fam miliyan 40 kawai  kungiyar zata iya kashewa a wannan kakar sai dai kuma sun bashi damar siyar da wasu daga cikin ‘yan wasan  kungiyar irinsu Ozil domin kashe kudin a kan sababbin ‘yan wasa.

Duka ‘yan wasan guda biyu dai Arsenal ta tayasu fam miliyan 37 bayan da kociyan ya bayyana Praet a matsayin wanda zai maye gurbin Aaron Ramsey wanda ya koma Jubentus yayinda kuma Joachim Andersen zai taimkawa  kungiyar a bangaren baya.

kungiyar  kwallon  kafa ta AC Milan ma ta nuna sha’awarta akan ‘yan wasan guda biyu sai dai  kungiyar Sampdoria ta bayyana cewa ‘yan wasan nata sunfi farashin da Arsenal ta taya su kuma suna bu katar  kari idan har anason su rabu da natasan ‘yan wasan

Arsenal dai tana fama da matsalar ‘yan wasan baya bayan da a wannan kakar aka zurawa  kungiyar  kwallaye da dama a raga sannan kuma akwai bu katar  kungiyar ta siyi wanda zai maye mata gurbin Ramsey wanda ya koma Jubentus a kyauta bayan kwantaraginsa ya  kare.

Exit mobile version