Connect with us

WASANNI

Arsene Wenger Ya Fara Tattaunawa Da Wata Kungiya A Kasar China

Published

on

Wasu rahotanni sun bayyana cewa mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger zai iya fin kowanne mai koyarwa daukar albashi a duniya  idan har ya amince zai koma kasar Sin wato China da koyarwa.

A satin daya gabata ne dai mai koyarwar ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar ta Arsenal bayan ya shafe shekaru 22 yana aikin koyar da kungiyar inda ya lashe kofuna da dama ciki har da gasar firimiya guda uku da kofin kalubale na FA guda bakwai.

Wenger yana karbar albashin fam miliyan takwas ne a shekara kusan rabin albashin da Pep Guardiola yake karba a Manchester City tun bayan zuwansa sai dai watakila zai iya kai fam miliyan 24 idan har ya amince zai koma kasar ta China.

Tsohon mai koyar da yan wasan tawagar kasar Italiya, Marcelo Lippi ne dai yake karbar albashi mafi tsoka a kasar China na fam miliyan 24 sai dai idan Wenger ya amince da komawa can din shima hakan za’a bashi.

Wenger dai yana son aiki da wata kungiyar a kasar Sipaniya sannan kuma yana komawa kasarsa ta Faransa domin cigaba da koyarwa yayinda kuma wani rahoton ya bayyana cewa yanason koyar da karamar kungiya ne domin yasa kungiyar nan ta girma ta kawo karfi.

A ranar 14 ga wata mai kamawa ne dai Wenger yace zai bayyana makomarsa a inda ake tunanin zai cigaba da koyar da kwallo a wata kungiyar amma a kasar China.
Advertisement

labarai