Kusan ‘yan Banga 10 ne suka rasa rayukansu yayin da ‘yan bindiga suka yi musu kwantan-ɓauna a dajin Mansur da ke yankin Duguri/Gwana a ƙaramar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi a ranar Lahadi.
‘Yan bindigar dai sun farmaƙi ‘yan Bangan da suka fito daga gundumomin Duguri da Gwana waɗanda suke kan aikin sintiri a yankin dazukan Duguri–Mansur–Dajin Mada, yankin da ya yi iyaka da jihar Bauchi da Filato ne, lamarin da ya janyo salwantuwar rayuwa.
- Za A Gudanar Da Taron Tallata Fim Din “Red Silk” A Moscow
- Kamfanin Sin Ya Kammala Ginin Cibiyar Horarwa Ta Hidimomin Yawon Bude Ido A Uganda
Majiyoyi daga yankin Duguri sun tabbatar ma wakilinmu cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu mutum huɗu ‘yan Duguri ne yayin da kuma wasu biyar suka kasance ‘yan yankin Mansur.
An labarto cewa harin ya wakana ne da safiyar ranar Lahadi kuma ‘yan bindigan sun yi awun gaba da shanu da sauran dabbobin al’umman yankin a yayin farmaƙin.
Kazalika, wakilinmu ya gano cewa baya ga ‘yan bijilante da suka rasa rayukansu akwai wasu fararen hula mazauna ƙauyen Sabuwar Sara su ma sun gamu da ajalinsu yayin da suke ƙoƙarin gudun neman tsira bisa harbe-harben ‘yan bindigan.
Sai dai bayanai sun tabbatar da cewa su ma ɓangaren ‘yan fashin dajin sun rasa mutanensu da dama da ake hasashen sun ma fi ‘yan Bangan mutuwa.
Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba ta bayyana haƙiƙanin adadin mutanen da suka rasa rayukansu a ɓangaren ‘yan Banga da ‘yan fashin ba.
A sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Litinin, kakakin rundunar , CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 05:40 a ranar 4 ga watan Mayun 2025, inda aka kai rahoton faruwar hakan ga shalkwatar ‘yansanda da ke Alkaleri da ƙarfe 09:40.
“Haɗakar ƙwararrun mafarauta daga gundumomin Duguri da Gwana a lokacin da suke aikinsu na sintiri a dajin Mansur, da Dajin Mada, iyaka da jihar Bauchi da jihar Filato, kwatsam sai suka ci karo da tawagar ‘yan fashin daji inda suka musu kwantan ɓauna domin farmaƙarsu,” Wakil ya shaida.
Ya ƙara da cewa bisa musayar wuta da aka yi a tsakaninsu, dukkanin ɓangaren sun raunata daga su kansu ‘yan Bijilante da kuma maharan.
Kakakin ya ce an tura jami’an ‘yansanda wurin da abun ya faru inda suka kwaso gawarwakin da aka kashe.
Binciken farko-farko na ‘yansansa shi ma ya tabbatar da cewa waɗanda suka rasu an samesu ne a dukkanin ɓangarorin biyu har ma wasu fararen hula daga ƙauyen Sabuwar Sara lamarin ya shafa a lokacin da suke neman tsira da rayukansu.
Sai dai, rundunar ta ce tunin aka ƙaddamar da bincike domin ganin an kamo ‘yan fashin dajin domin tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama’a.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi tur da harin tare da tura jami’ai domin su gana da al’ummar kauyen Mansur domin neman hanyoyin da za a inganta tsaro.
Ya jajanta wa iyalan wadanda aka kashe inda ya ba su tabbacin nema musu adalci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp