Connect with us

DAGA NA GABA

Asadul Muluuk (6)

Published

on

Hafida ta ce; “Ki gaya masa ya yi hakuri za mu zo,” Daya daga cikinsu da ake kira Yus’feerah ta ce; “Sai ki hanzar ta ki yi shiri ki fito mu isa gareshi.” Hafida ta kalleta shekeke ta ce; “Yus’feerah hanzari kuma? Ai babu sauran hanzari, dole ne yayi hakuri da halinmu, sai kuma yadda muka yi da shi, bari ki gani.” Sai ta tashi ta shiga daki ta fara shiryawa.
Sa’adda Layusa ta isa gareshi sai ta bashi masauki, daga baya ta kawo masa kayan ciye-ciye da na sha, da ta ga ya zauna sai ta fito ta nufi wurin dokinsa, shi ma ta kare masa kallo kana ta koma cikin gida ta same su.
Shahida ta kalle ta, ta ce “Kafin ki ce komai je ki dauko min tawada da alkalami da takarda da zan yi zane.” Layusa ta je ta kawo, daga nan Shahida ta ce; “To mu je ki fara karanta min ni kuma zan zana shi da duk abin da ya zo da shi. Daga nan ta fara tambayar Layusa, ya kai misalin shekaru nawa, ya ya launin jikinsa yake, ya ya shakalin jikinsa ya ke, wane irin kaya ya sanya, na Sarauta ne ko kuwa, dan gari ne ko bako, mayaki ne ko ba fatake ne, a wane irin doki ya zo?”
Layusa ta gyara zama ta ce; “Saurayi ne duka-duka shekarun ba su fi ishirin da bakwai ba, Fatar jikin sa launi jikinmu ce, yana da tsayi dai-dai kwatance tare da barage, yana fuska cikakkiya mai kyau. Sanye ya ke da fararen kaya dogwaye masu ratsin kore, ya yi nadin rawani kuri.
A jikin dan yatsarsa ta hagu akwai wani zobe na danyar a zurfa kirar Askandariyyah, babu takalmi a kafarsa, sai dai Huffi dan kasar Habasha. Yana rike da carbi dan kasar Yasriba mai launi kankara adadinsa talatin da uku, na ga bakinsa ya na motsi kamar cewa shi yana tasbihi ne. Turaren da ya shafa kuma Ash shaamee ne, da ake sarrafa shi daga itaciyar Shamhuur.
Sai kuma dokinsa, fari ne mai yarfen fatsi-fatsi, ingarma ne kiwon Tirkawa, sirdin kuma kirar kasar Hindu, shimfidar kan dokin kuwa kirar kasar Sin ce. Sai linzamin dokinsa da kaiminsa duk kirar kasar Habasha, wannan shi ne abin da ya inganta a cikin suffofin bakonku da na dokinsa.”
Tana gama fadar haka, Shahida ta nuna mata hoton, ga shi a zane, da Layusa ta karba ta duba mamaki ya rufe ta, saboda ta ga yadda zanen yake kai ka ce dama ta sanya shi a gaba ne ta na kallon sa tana zanawa.
A dai-dai wannan lokacin kuma Hafida ta fito daga wanka, Shahida ta nuna mata, “Kin ga surar bakonki.” Ko kallon wurin ba ta yi ba ta ce; “Rashin abin yi kenan ki zauna kina zana surar wani saurayi.” Tun da Shahid ya zauna yake sake-sake a zuciyarsa dangane da yiwuwar zamansa ko akasin haka, amma dai yana kokarin ya cika alkawarin da ya daukar wa abokinsa na cewar zai yi hakuri a bisa duk abin da za’ayi masa, sannan kuma yana duba lokacin Sallar Juma’a wanda hakan ya fi komai muhimmaci.
Har yanzu dai Hafida ba ta gama shiryawa ba, kawayenta sun gaji da magana akan rashin fitarta da wuri, ga kuma lokacin masallaci yana dada karatowa.
Dai-dai lokacin da suke fitowa daga cikin gida, shi kuma ya fito daga in da aka sauke shi, yana fitowa sai ya hango su daga nesa, sai dai bai kai ga fahimtar ko wacce daga cikinsu ba. Tun da ya kalle su sau daya bai sake kallonsu ba, da zuwa wurin dokinsa bai yi wani jira ba yayi addu’a ya hau yayi tafiyarsa.
Ko da karasowarsu suka iske baya nan. Hafida ta tambayi Layusa me ya ce; “ Layusa ta amsa cewa; “Ya fada min lokacin zuwa Masallaci yayi, don haka shi ya tafi Sallar Juma’a.” “Bai gaya miki lokacin da zai dawo ba?” “Lala bai gaya min ba.”inji Layusa. Hafida ta ce; “Kaicon wayonki na rashin kan gado da har zaki kasa tambayar bako abin da ya dace.”
Shahidah ta ce; “Ya kamata ki fara kaicon halinki na rashin girmama bako, kina nuna izza da mutakabbiranci wai don Saurayi ya zo wurinki, kullum cikin zagin samari da kushe su kike, kuma kin fi kowace a cikin mu son Saurayi, don baki da abin karantawa sai labaran soyayya.”
Ta yi tsaki suka koma cikin gida, komawarsu cikin bacin rai suka sake hawanta da fada, “Ai ga irinta nan kin je kin zauna kina kwalliya kamar za ki sauya halittar jikinki, yanzu wa yayi asara? Nan gaba idan an sake zuwa wurinki ki zauna kwalliya,” Hafida tana magana cikin sanyin jiki ta ce; “Haba kawayena so kuke da zarar an ce ana son mu kawai mu mika wuya, ba za mu nuna isar mu ta ‘yan mata ba?” Sauma’iyyah ta ce; “kaicon wannan ra’ayi naki, ta yaya mutum zai zo wurinki tun misalin lokacin walha, amma har lokacin Sallar juma’a ya shigo baki saurare shi ba, wacece ke daga cikin matan duniya?
Wannan shi ne sakamakon Mutakabbiri,”
“Kash! kun yi wa lamarin mummunar fahimta, hakan fa ba shi ne abin da yake cikin zuciyata ba, kuma me ya hana ku bani shawarar kaucewa haka tun da fari?” A’ah sau nawa Yusfeerah za ta gaya miki kika kau da kai? wa kika fi kyau a nan ko asali? “Haba Shahidah da wanne kuma za ta ji?” inji Faheesah. Shahidah ta ce; “Ta ji da kowanne ma ai ita ta jawo.” “Wannan dai ya wuce sai a kiyayi gaba, mu ma kuma mu yi hakuri.” Inji Sha’eeratu. Shahida ta ce; “Ai na san ba zai jima ba zai dawo, kuma za mu dinga ziyartar ki sa’i-sa’i, ni dai na koma gida.”
Shi kuwa Shahid bayan ya dawo daga juma’a ya wuce gida ya ci abinci, kana ya kwanta yayi bacci, da lokacin sallar La’asar ya yi sai ya tashi bisa isharar tsuntsunsa Hafir ya je ya ba da farali.
Hafir wani aku ne da Shahid ya karbe shi a wurin mahaifinsa, a duk sa’adda yake bukatar a tashe shi daga bacci shi ne yake tashinsa, haka zalika idan yana bukatar ya tuna masa wani da zai yi, to sai ya gaya wa Hafir, shi kuwa da lokacin ya yi sai ya tuna masa da irin yanayin da zai gane.
Bayan an yi Sallar La’asar ya wuce zuwa gidan Sarki, don ya sanar da Samir abin da ya faru, da ya same shi suka zauna Samir ya dube shi “Shahid na ga fukarka da alamar damuwa,” Shahid ya ce; “A a daga bacci na tashi, amma dai akwai damuwa, sai dai damuwar kadan ce tunda ka fini sanin abin da zai faru, kuma dama ka fada min kafin afkuwarsa.
Na je wurin Hafida tun kusan lokacin Walha, amma ban samu ganin ta ba, har lokacin Sallar juma’a, da na ga lokaci yayi na hakura na dawo gida.”
“Wannan kadan kenan daga cikin halinta kamar yadda na ambata maka.” Na bar mata sakon tafiyata, duk da ban fadi ranar da zan koma ba, amma dai nan da makonni biyu zan koma, sannan na san ta fidda rai da zuwana.” Wannan shi ne lamarin Samir da abokinsa Shahid.
Ita kuwa Hafida, kullum sai ta yi kwalliya mai tsananin kyau, sannan a ko da yaushe dakinta a cike yake da kawaye don sauraron dawowar bakonta, amma ina shiru babu labarinsa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: