• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Askarawan Zamfara Da Aka Kashe Sun Nuna Sadaukarwa, Za Mu Kula Da Iyalansu – Gwamna Dauda

-Ya Ce Ba Za Su Sarara Da Fatattakar 'Yan Bindiga A Jihar Ba

by Leadership Hausa
1 year ago
zamfara

Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin gwamnatinsa za ta bayar da cikakkiyar kulawa ga iyalan jami’an Askarawan Zamfara da aka kashe a wani kwanton ɓaunar da aka yi masu.

Gwamnan ya yi wannan alƙawarin ne a fadar ‘Yan Doton Tsafe lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan jami’an Askarawan Zamfara da ‘yan bindiga suka yi wa kwanton ɓauna a cikin makon da ya gabata.

Yayin jajanta wa masarautar da kuma Iyalan waɗanda aka kashen, Gwamna Lawal ya nuna cewa wannan sadaukarwa da jami’an suka yi, ba za ta tafi a banza ba.

  • Yunkurin Magance Matsalar Tsaro Da Rigingimu A Arewa…

A cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Gusau, Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya ambato Gwamna Lawal yana cewa: “Na zo nan yau ne domin in miƙa ta’aziyyata ga masarauta, iyalai da al’ummar Tsafe bisa kisan da aka yi wa gwarazan mu, a wani kwanton ɓauna da aka yi masu.

zamfara

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

“Wannan wani bala’i ne wanda muka ji raɗaɗin sa matuƙa. Lallai mun shaida wannan tsayin-daka na waɗannan dakaru don kare rayukan al’ummar su.

“Ina jin wannan baƙin labari, sai na turo da wata ƙaƙƙarfar tawaga ta gwamnati, ƙarshin jagorancin Mataimakin Gwamna domin su zo su miƙa ta’aziyya ga masarauta da iyalan waɗanda abin ya shafa.

zamfara

“Ina tabbatar maku da cewa irin waɗannan abubuwan, ba za su dakatar da mu daga farmakin da muke kai wa ‘yan bindiga ba. Muna yin duk abin da ya wajaba wajen kawo ƙarshen ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

“Gwamnatin jihar Zamfara za ta ɗauki duk ɗawainiyar iyalan waɗannan Asakarawan. Ina yin wannan alƙawari ne a nan, kuma za mu tabbatar mun cika shi.

Nan take kuma Gwamnan ya bayyana bayar da tallafin kuɗaɗe da kayan abinci ga iyalan mamatan.

A jawabin da ya gabatar, Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa, ya nuna godiyar sa ga Gwamna Lawal, da kuma jijina masa bisa irin namijin ƙoƙarin da ya ke yi wajen samar da tsaro da jin daɗin al’umma.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Tsaro

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
Tsaro

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
Tsaro

Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22

October 12, 2025
Next Post
Yadda Muka Sanya Tinubu Ya Soke Kwangilar Aikin Hanyar Kankara Zuwa Katsina inji Ibrahim Masari 

Yadda Muka Sanya Tinubu Ya Soke Kwangilar Aikin Hanyar Kankara Zuwa Katsina inji Ibrahim Masari 

LABARAI MASU NASABA

Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

Me Aka Gano Kan Makomar Tattalin Arzikin Kasar Sin Daga Karuwar 5.2% Na Tattalin Arzikinta?

October 21, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni

October 21, 2025
Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

Jirgin Kasa Mafi Saurin Gudu A Duniya Ya Fara Zirga-Zirgar Gwaji A Sin

October 21, 2025
Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan ₦2.3 Ga Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalansu

Ma’aikatan Manyan Makarantu Na Kaduna Sun Dakatar Da Yajin Aiki Yayin Da Gwamna Sani Ya Amince Da Sabon Tsarin Albashi

October 21, 2025
Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia

October 21, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Wata Tankar Mai Ta Sake Fashewa A Neja

Da Ɗumi-ɗumi: Fashewar Tankar Man Fetur Ta Yi Ajalin Rayuka 30 A Neja

October 21, 2025
Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia

Sin Ta Bayar Da Tallafin Dala Miliyan 3.5 Ga Shirin Samar Da Abinci A Zambia

October 21, 2025
Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya

Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya

October 21, 2025
An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

October 21, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.