Yayin da Isra’ila ke kai wa sojojin Hamas da Gaza hari ba ji ba gani, ana iya ganin irin yadda yakin ke ta’azzara da kuma yadda ake samun asarar rayuka musamman ma a Gaza. Amma Babbar barazana ga Isra’ila ita ce ta Hezbollah, kungiyar Mayaka ko kuma masu fafutukar siyasa da suke da yawa da kuma karfi a kasar Lebanon kuma su kai iyaka da Isra’ila ta Arewacin kasar.
Kungiyar mayakan Hamas da Hizbullah suna samun goyon bayan Iran, wanda kuma su dukkansu suna da buri da yunkurin ganin sun darkusar ko kwatar kansu daga Isra’ila.
Wannan matsayi suna daukarsa a matsayin babban muradinsu.
Duk kungiyoyin mayakan biyu suna da bambance-bambance irin nasu da kuma manufofin kafa su, wannan shi ne ya janyo rashin tasirin kungiyar mayakan Hezbollah kan yakin da kungiyar mayakan Hamas ke yi da Isra’ila.
Kungiyar Mayakan Hizbullah
Hizbullah wacce kalmar Larabci ce da ta ke nufin ” Kungiyar Allah “. Kungiyar tana daukar kanta a matsayin wani bangare na akidun Shi’a. Akidar Shi’a tai kaurin suna wajen da mayar da hankali kan kora tare da sukar Turawan Yamma da kuma masu mara mata baya irin su Amurka. Sannan tana cikin kasashen da suke gaba-gaba wajen kin amincewa da Isra’ila a matsayin kasa.
Tarihinsu
An kafa kungiyar ne a shekara ta 1982, lokacin da ake tsaka da yakin basasar Kasar Lebanon wanda aka shafe shekaru 15 ana yinsa. Bayan da Isra’ila ta mamaye Kasar Lebanon a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da bangarorin Falasdinawan da ke Lebanon suka kai mata, hakan ya sa aka samu kafuwar kungiyar Kuuma ta samu goyan bayan Iran, musamman ma daga dakarun da suka taimaka wajen juyin-juya halin kasar, inda suka taimaka musu da kudade, makamai da horo a kokarin fadada tasirin Iran a cikin kasashen Larabawa.
Kungiyar Sojojin Hizbullah ta ci gaba da samun ci gaba bayan kawo karshen yakin basasar Lebanon a shekarar 1990, duk kuwa da yadda akasarin kungiyoyin da suka taka rawa a yakin basasar sun suka kwance damara. Kungiyar ta ci gaba da mai da hankali kan ‘yantar da ‘ Labanon daga Isra’ila, kuma ta shafe shekaru da yawa tana yakin basasa da sojojin Isra’ila da suka mamaye Kudancin Lebanon har zuwa lokacin da Isra’ila ta fice a shekara ta 2000.
Daga nan sai kungiyar Hizbullah ta mayar da hankali sosai wajen kwato yankin da ake takaddama a kan iyaka na gonakin Shebaa na Lebanon .
A shekarar 2006, Hizbullah ta shiga yakin makwanni biyar da Isra’ila a wani yunkuri na ‘yantar da Falasdinu. Rikicin da ya janyo asarar rayukan Isra’ilawa sama da 158 da kuma ‘yan Lebanon sama da 1,200, galibi fararen hula.
Daga shekarar 2011, lokacin yakin basasar Kasar Syria, karfi da tasirin kungiyar Hizbullah ya kara bayyana, saboda yadda dakarunta suka taimaka wa shugaban Syria Bashar al-Assad, wanda ke kawance da Iran, a kan galibin ‘yan tawayen da suke da akidar Sunni.
A shekarar 2021, shugaban Kungiyar Hizbullah, Hassan Nasrallah ya ce kungiyar na da mayaka 100,000.
Kungiyar Hizbullah na taka rawa a matsayin jam’iyyar siyasa a Lebanon. A shekara ta 1992 ne aka fara zaben wakilai takwas a majalisar dokokin kasar Lebanon. To sai dai kuma a shekarar 2018 kungiyar Hizbullah ta samu rinjaye a majalisar kasa inda ta kafa gwamnati.
Kungiyar Hizbullah ta ci gaba da rike kujeru 13 a zaben shekara ta 2022 amma kawancen ya rasa rinjayen da yake da shi kuma kasar a halin yanzu ba ta da cikakkiyar gwamnati mai aiki . Sauran jam’iyyun na Labanon na zargin kungiyar Hizbullah da gurgunta gwamnati da zagon kasa da kuma taimakawa wajen ci gaba da zaman lafiyar kasar Labanon.
Kungiyar Mayakan Hamas
Hamas, itama kalamar Larabci ce da ake fassara ta da “Kishi” wanda kuma kungiyar mayakan Hamas ke fassara ta “Juriya kan Musulunci”. An kafa kungiyar ne a shekarar 1987, a Gaza, a matsayin reshe na kungiyar ‘yan uwa Musulmi, karkashin jagorancin wata fitacciyar kungiyar Sunni da ke da cibiya a Masar.
A farkon lokaci, kungiyar Hamsa tana alla wadai ne da tofin ala tsine ga Isra’ilawa kan irin mamayar da suke musu da kuma yunkunrinsu na gallaza musu da kuma tauye musu hakkinsu.
Siyasar Falasdiwa ta sauya sosai bayan yarjejeniyar Oslo a shekarar 1993, da kuma wasu jerin yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin gwamnatin Isra’ila da kungiyar ‘yantar da Falasdinu (PLO) a matsayin cikkakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya.
Saboda rashin gamsuwa da kuma adawa da waccar yarjejeniyar, wani bangare na Kungiyar Hamas masu dauke da makamai, na Al-Kassam Brigades, ya balle tare da tabbatar da kansu a matsayin babbar rundunar juriya da yaki da kasar Isra’ila.
Bangaren kungiyar ya fara kai hare-hare da kunar bakin wake (2000-2005), kafin kungiyar ta fara amfani da makaman roka.
Kamar Hizbullah, Hamas na ganin kanta a matsayin jam’iyyar siyasa, ta shiga tare da lashe zabbn ‘yan majalisar dokoki a shekarar 2006, da kuma shekarar 2007, ta sami iko da yankin Zirin Gaza a wani kazamin fada da jam’iyyar Fatah wanda suke gaba da juna, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 100.
Hamas dai na rike da yankin Gaza tun daga lokacin, inda ta nuna rashin hakuri da ‘yan adawar siyasa. Ba su taba gudanar da zabe ba, kuma ana kama abokan hamayyar siyasa da masu suka.
A tsawon wannan lokaci, reshen Hamas da ke dauke da makamai ya kara samun kwarewa, tare da samun makamai, wanda suka hada da roka, bindigogi masu sarrafa kansu da dai sauaransu.
Yaya Hamas da Hizbullah suka bambanta?
Hamas dai na samun tallafin kudade da makamai da horarwa daga kasar Iran, amma ba a aljihun Iran din ba kamar yadda kungiyar Hizbullah ta ke samun goyon bayan Iran kadai, kuma tana karbar umarnin daga wajenta.
Sabanin haka, Hamas ta samu tallafi a baya daga Turkiyya da Katar, da dai sauransu, kuma tana gudanar da ayyukanta na cin gashin kai. Haka kuma kungiyar ta dade da rashin jituwa tsakaninta da Iran dangane da sabanin ra’ayinsu a Siriya.
A yanzu dai wannan yaki ne tsakanin Isra’ila da Hamas. Har yanzu dai Hezbollah na zama barazana ga Isra’ila. Idan Iran ta kunna ta, cikakken shigarta zai canza yanayin rikici cikin sauri kuma zai iya bude yakin yanki.