Asarar Da Ta Sa ‘Yan Albasa Yanke Kai Kaya Kudu Maso Gabashin Nijeriya 3rd

Albasa

Daga Yusuf Shuaibu

A ranar Litinin ce, Kungiyar Manoman Albasa da Kasuwancinta (OPMAN) ta bayyana irin dimbin asarar da ta tafka wadda ta tilasta mata dakatar da kai albasa yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya.

Da yake zantawa da manema labarai a Jihar Sakkwato a ranar Lahadi, shugaban kungiyar Aliyu Isa ya bayyana cewa, “idan gwamnati ta gaza cimma bukatun kugiyarmu, to za mu dakatar da kai albasa yankin Kudu maso Gashin kasar nan tun daga ranar Litinin, 7 ga watan Yunin shekarar  2021.

“Lokacin zanga-zangar EndSARS, an farmaki mambobin kungiyarmu da dama.

“A Shaha mun rasa rayukan mambobinmu guda 27 da tireloli guda biyar da buhunan albasa 5,600 da kananan motocin 12 da sauran dinbin dokiyoyi,” in ji shi.

Isa ya kara da cewa, sun tafka asarar kudaden albasa wanda suka kai na naira biliyan 4.5 da dinbin dokiyoyi da wadanda ake zargin ‘yan daba da ke Kudu maso Gabashin Nijeriya suka lalata a watannin da suka gabata, kari a kan mambobin kungiyar da aka kashe ba tare da biyan kudin fansa ba.

 

Kungiyar ta lissafa abubuwan da ta tafka asara lokacin rikicin Aba a Jihar Abiya da Shasha da ke Jihar Oyo da kuma karamar hukumar Mbaise cikin Jihar Imo, inda ta bayyana cewa ta rasa mambobinta guda uku da tireloli 30 da kananan motoci guda tara da sito 50 da buhun albasa guda 10,000 da sauran dokiyoyi masu yawa. Kungiyar ta ce a Jihar Imo, ta rasa tireloli guda biyu wanda kudinsu ya kai na naira 13,000,000 a watan Fabrairu.

 

“A kan wadannan matsalolin ne muka dauki matakin dakatar da kai kayayyakin abinci jihohin Kudancin kasar nan a watan Fabrairu ta hanyar kungiyar hadaka.

 

“Bayan da mambobin zantarwa na wannan kungiya suka kammala tattaunawa tare da rashin daukan mataki daga wajen gwamnati a kan mayar da murtani, shi ya sa muka dauki wannan mataki,” in ji Isa

Haka kuma Isa ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su taimaka musu domin gudanar da kasuwancinsu yadda ya kamata ba tare da tashin hankali ba.

“Muna bukatar gwamnatocin jihohi da gwamnatin tarayya da su dawo da doka da oda a dukkan jihohin kasar nan.

“Haka kuma muna kira ga mutanen yankin Kuduncin Nijeriya da su bari Hausawa su zauna lafiya, domin mun kasance ne a cin saboda gudanar da harkokin kasuwanc i cikin zaman lafiya.”

Ya kuma yi kira da gwamnatocin jihohi da su hada kai da gwamnatin tarayya wajen kafa kwamitin binciken lamarin da ya janyo rasa rayuka da dokiyoyin mambobin kungiyarsu.

 

 

Exit mobile version