Asusun UNICEF Ya Bukaci Gaggauta Sakin Daliban Islamiyyar Da Aka Sace A Neja

Daliban Islamiyya

Daga Yusuf Shuaibu,

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bukaci a gaggauta sako daliban Isilamiyar guda 150 da aka yi garkuwa da su na makarantar yara ta Salihu Tanko Islamiya da ke Tegina cikin karamar hukumar Rafi ta Jihar Neja, wanda wasu daga cikinsu yarane kanana.

A cikin wata sanarwar da UNICEF ya fitar ga manema labarai a garin Bauchi ranar Litinin, ta bayyana cewa, “an kwashe tsawan makonni biyu ke nan da yin garkuwa da daliba 150 na makarantar Isilamiyyar Salihu Tanko da ke Tegina cikin karamar hukumar Neje a yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya, dole ne a gaggauna sako wadannan yara.

“Mun shiga firgici na tsawan makwanni biyu bayan sace diliban guda 150 daga makaranta, wanda har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane,” in ji babban jami’I Rushnan Murtaza da ke wakiltar UNICEF a Nijeriya.”

UNICEF ya kara da cewa iyayan yara da ‘yan’uwa da abokan arziki na iyalan wadannan yara sun kadu ganin yadda ba su san halin da ‘ya’yansu suke ciki ba a hannun ‘yan bindar da ke garkuwa da su.

“An farmaki wadannan yara ne a makarantarsu, inda wasu ma ba su kai shekaru uku ba. Mun yi mamakin yadda wannan lamari yake faruwa a Nijeriya wanda yana iya taba lafiyar yaran da aka sace,” in ji UNICEF.

Haka kuma UNICEF ya bayanna cewa farmakin daliban makaranta yana janjo raunata harkokin karatun yara. Ta bukaci gwamnatin Nijeriya da ta dauki matakan da za su bayar da kariya ga dukkan makarantu da ke cikin kasar. Murtaza ya bayyana cewa ya kamata makarantu su kasance wajen da ya fi samun tsaro, amma bai kamata a samu farmaki a makarantu ba, domin waje ne da ke da matukar mahimmanci ga karatun yara.

 

Exit mobile version