Connect with us

LABARAI

ASUU Ta Koka Kan Yawaitar Jami’o’i A Nijeriya

Published

on

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta zargi Gwamnatin Tarayya da ta Jihohi da yawaitar jami’o’in kasar nan.

Farfesa Biodun Ogunyemi, Shugaban kungiyar Malaman Jami’a Na kasa (ASUU), ya bayyana damuwar su a wani taro da aka gudanar ranar Asabar a garin Jos.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, taron an gudanae da shi ne a zauren majalisar, wanda Jami’ar Jos ta shirya a sashen kungiyar, a cewar shugaban, gwamnatocin tarayya da jihohi suna kafa Jami’o’i ba tare da biyan su isassun kudade ba, ya kara da cewa wasu daga cikin jami’o’in da aka kafa ba a da bukatarsu.

“Gwamnatocin tarayya da jihohi suna kafa jami’o’i ba tare da basu cikakken kudade ba, misali, me ya sa muke bukatar Jami’ar sufuri, ko ta Fasahar Sadarwa da bayanai (ICT)?

“Duk wadannan jami’o’in idan an samar da su gwamnati na iya ba su kulawa.

Don haka samun yawaitar Jami’o’i ba zai taimka mana da komai ba, kuma wannan ita ce babbar illa ga kasar nan,” in ji shi.

Ogunyemi ya ci gaba da nuna takaicin cewa gwamnatocin jihohi sun mai da kafa jami’o’i a matsayin tsarin mazavu, maimakon cibiyar samar da ci gaba.

Ya nuna damuwa tare da matukar bakin cikin cewa idan ba a kula da kyau ba, ilimin jami’a a kasar zai shiga cikin wala-wala kamar yadda yanzu yake a tsarin ilimin firamare na yanzu.

Abin da muke gani a yau shi ne, gwamnatocin jihohi sun karkatar da kafa jami’o’i zuwa tsarin gudanar da zaven gundumomi; ta yadda za ka ga kowane gwamna yana son samun jami’a a mazavarsa.

“Wannan abin bakin ciki ne kwarai da gaske, kuma idan ba mu yi hankali ba, ilimin jami’a zai rushe kamar makarantun firamaren gwamnati na kasar nan.

“Don haka, abin da ASUU take matukar fafatawa a kansa shi ne dakatar da rushewar ilimi baki daya.

Bukatun mu ba muna fada ne domin son kai ba, ”in ji shi.

Ogunyemi ya shawarci gwamnatin tarayya da ta gyara jami’o’in gwamnati, yana mai cewa ta hanyar yin hakan, irin wadannan cibiyoyin za su iya zama masu samar da hanyoyin samun kudaden shiga.

Ya bukaci gwamnati da ta aiwatar da shawarar kungiyar bisa la’akari da rahoton lissafi na 2012 da sauran bukatun kungiyar.
Advertisement

labarai