Kungiyar kwallon kafa ta Athletico Madrid ta buga canjaras da abokiyar karawarta Real Sociedad a wasan sada zumunci da suka buga.
Kungiyar ta Madrid na shirye shiryen tunkarar kakar wasa ta badi inda a bara ta kare a mataki na biyu yayinda Fc Barcelona ta lashe Kofin gasar kalubale ta Laliga.
- Fitaccen Malamin Musulunci Dokta Ismail Surty, Ya Rasu A Birtaniya
- Sojojin Nijar Sun Tir Da Takunkuman Da ECOWAS Ta Sanya Musu
A minti na 82 dan wasan kasar Holland Memphis Depay ya samu bugun daga kai sai mai tsaron raga amma golan Sociedad Unai Marero ya hanata shiga.
Kocin Athletico Madrid Diego Simeone ya bayyana wannan wasa a matsayin somin tabi inda yace yan wasansa sun shirya tsaf domin tunkarar gasar badi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp