ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Atiku Da Wasu Sun Kafa Sabuwar Jam’iyya, Sun Nemi INEC Ta Musu Rajista

by Sadiq
6 months ago
Atiku

Manyan shugabannin haɗakar adawa a Nijeriya, ciki har da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, sun haɗu don kafa sabuwar jam’iyya mai suna All Democratic Alliance (ADA). 

Sun ce za su yi amfani da wannan sabuwar jam’iyya wajen ƙalubalantar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

  • Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (6)
  • Sin Ta Jadadda Wajibcin Daukar Jerin Matakan Magance Matsalar Talauci Da Karancin Ci Gaba Da Rikici

Ƙungiyar, wadda ke aiki ƙarƙashin Nigeria National Coalition Group (NNCG), ta riga ta gabatar da buƙatar yin rijista da sabuwar jam’iyyar ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).

ADVERTISEMENT

Sun aike da takardar neman rijistar ne a ranar 19 ga watan Yuni, 2025, kuma INEC ta karɓa a hukumance a ranar 20 ga watan Yuni.

Shugaban jam’iyyar ADA, Cif Akin Ricketts, da Sakataren rikon ƙwarya, Abdullahi Musa Elayo, ne suka sanya hannu a takardar.

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

A cikin takardar, ƙungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar kafa sabuwar jam’iyya maimakon haɗaka da wasu.

Sun bayyana cewa sun zaɓi suna All Democratic Alliance (ADA) kuma taken jam’iyyar shi ne “Justice for All” wato “Adalci ga Kowa.”

Sun kuma haɗa da adireshin babban ofishin jam’iyyar a cikin takardar.

Sun gabatar da wasu muhimman takardu da suka haɗa da tambarin jam’iyya, tsarin kundin mulki, tutar jam’iyyar, da manufofinta.

Tambarin jam’iyyar ya ƙunshi kayan hatsi irin su masara da launuka masu ma’ana.

Kundin tsarin mulki kuma ya ƙunshi manufofi, tsari da dokokin jam’iyyar, bisa ga tsarin dokokin Najeriya da ƙa’idar dimokuraɗiyya ta duniya.

Takardar ta ƙare da girmamawa, inda ta ke roƙon INEC da ta ɗauki mataki na gaba wajen kammala rijistar jam’iyyar.

Sauran manyan ‘yan siyasa da ke cikin wannan haɗaka sun haɗa da Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark, da Dakta Umar Ardo, wanda ya kafa ƙungiyar League of Northern Democrats.

A baya, ƙungiyar ta yi la’akari da shiga wata jam’iyya, kamar African Democratic Congress (ADC) da Social Democratic Party (SDP).

Sai dai daga sun fasa bayan sun lura da rikice-rikicen cikin gida da shari’o’i da waɗannan jam’iyyu ke fuskanta.

Saboda haka, suka zaɓi kafa sabuwar jam’iyya da za su fara daga tushe tare da daidaita tsakanin mambobinta.

Yanzu suna jiran matakin da INEC za ta ɗauka yayin da suke shirin tunkarar zaɓen 2027.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Next Post
Me Ya Kamata Mai Yaron Ciki Ta Kula Da Shi?

Me Ya Kamata Mai Yaron Ciki Ta Kula Da Shi?

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.