Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana gazawar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu yayin da ta cika shekaru biyu a mulki, yana mai zargin gwamnatin da jefa Nijeriya cikin mawuyacin halin bashi da talauci.
A cikin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, Atiku ya siffanta gwamnatin Tinubu a matsayin “wacce ba ta da ƙwarewa, ba ta da alaƙa mai kyau da jama’a, kuma wacce ba ta da tausayi ga talakawa.” Ya ƙara da cewa babu wata gwamnati da ta taba haddasa irin wannan wahala ga ‘yan ƙasa ba tare da nuna gaskiya da riƙon amana ba.
- Hadin Gwiwar Sin Da Yankin Turai Na Kara Kawo Haske Ga Tattalin Arzikin Duniya
- Buhari Ya Yabi Tinubu, Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Rage Tsammani Da Dogon Buri
Atiku ya ce gwamnatin Tinubu ta ƙara yawan talauci, ta kuma kafa tarihin cinye kuɗin jama’a ba tare da wani aiki ba. Ya yi nuni da rahoton 2024 yunwa na duniya inda Nijeriya ta fi Sudan yawan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki. Haka kuma, ya soki ƙarin kuɗin rajistar katin ɗan ƙasa da ƙaruwar kuɗin makarantu a jami’o’in gwamnati.
A cewarsa, bashin da gwamnatin Tinubu ke ci yanzu ya kai Naira tiriliyan 144 daga Naira tiriliyan 49 da ya gada a 2023 – ƙarin kashi 150 cikin dari. Ya bayyana cewa shirin ci gaba da karɓar bashin har dala biliyan 24 zai iya kai bashin ƙasar Naira tiriliyan 183, abin da ya kira “cin amanar ƙasa.”
Atiku ya yi gargaɗi cewa Nijeriya na cikin haɗarin faɗawa cikin “bautar bashi”, yana mai kira ga ‘yan majalisa, da ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai da su tashi tsaye. Ya kuma lashi takobin gina ƙawance hamayya mai ƙarfi domin hana karkata ƙasa zuwa jam’iyya ɗaya da take zaluntar masu adawa da ci gaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp