Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Abubakar Atiku, ya bukaci kotun koli ta soke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPC) ta yanke, wadda ta tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
A cikin kunshin daukaka karar da Atiku ya shigar a gaban kotun koli, ya gabatar da hujjarsa a kan wasu dalilai 35, inda ya dage cewa kotun zabe a hukuncin da shugabanta, Mai shari’a Haruna Simon Tsammani, ya yanke, ta aikata babban kuskure da rashin adalci a sakamakon binciken da ta kammala.
- Atiku Da Obi Sun Yi Fatali Da Hukuncin Kotun Kararrakin Zabe Sun Nufi Hanyar Zuwa Kotun Koli
- Yadda Tinubu Ya Yi Nasara Kan Abokan Hamayyarsa Atiku Da Obi
A cikin karar da ke kalubalantar ayyana Tinubu a matsayin shugaban kasa da INEC ta ayyana.
Daukaka karar wadda babban lauyan Atiku, Cif Chris Uche, SAN, ya shigar, ya bukaci kotun koli da ta yi watsi da duk wani bincike da yanke hukuncin da kotun ta yanke kan cewa ba su fahimcu gaskiyar dalilin karar da ya shigar ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ci gaba da cewa kotun ta yi kuskure a doka, kan kasa soke zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 bisa dalilan rashin bin dokar zabe ta 2022.