Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kaddamar da makarantar haddar Al-Kur’ani a garin Gunduwawa da ke karamar hukumar Gezawa a Jihar Kano.
Makarantar Al-Kur’ani da Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya gina ta samu sunan kakansa, Gwani Mammadu Dan Gunduwawa.
- “Jarumi Adam A Zango Bai Saki Matarsa Ba”
- Canjin Kudi: Dole Ne Mu Ceto Tattalin Arzikin Nijeriya Daga Durkushewa —Matawalle
Makarantar za ta dauki nauyin karatun dalibai maza 250 da mata 250 a lokaci guda, kuma daliban za su haddace kur’ani mai tsarki cikin watanni shida.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da makarantar, Wazirin Adamawa ya yaba wa Sanata Shekarau bisa kaddamar da aikin wanda zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa ilimin Addinin Musulunci.
Tsohon mataimakin shugaban kasar dai ya je Kano ne domin gudanar da gangamin yakin neman zabensa da aka shirya gudanarwa a gobe.
A nasa bangaren, Sanata Shekarau da ke cike da murna, ya gode wa Atiku Abubakar bisa kaddamar da aikin.
Shekaru ya kuma bayyana cewa, a ko da yaushe ya himmatu wajen samar da ribar dimokuradiyya ta hanyar ayyukan da za su taba rayuwar al’umma.