Wata kungiya da aka yi wa lakabi da (TAM) mai goyon bayan takarar Atiku Abubakar a 2023, ta nesanta shi daga rikicin cikin na jam’iyyar PDP a jihar Ekiti.
Wasu a jihar na hasashen cewa rikicin ba zai rasa nasaba da tsamar siyasa da ke a tsakanin Atiku da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, wanda ya kasance aminin siyasar tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ba.
- ‘Yan Sanda Sun Cafke Barayin Ragon Layya 2 A Ogun
- Yadda Muka Ji Rugugin Makamai Ta Ko Ina A Yayin Harin Fasa Gidan Yarin Kuje – Wasu Fursunoni
In za a iya tunawa, wasu ‘ya’yan kwamitin zartarwa na PDP da ke biyayya ga Fayose a ranar Litinin da ta wuce sun zabi Alaba Agboola, wanda kuma sananne ne wajen yin biyayya ga Sanara Biodun Olujimi, don cike gurbinsa da tsohon shugaban jam’iyyar jihar, Bisi Kolawole.
Har ila yau, a wata ganawa a garin Ado da wanda ke yakar Fayose a cikin kwamitin zartarwar an zabi tsohon shugaban karamar hukumar Ado Ekiti a matsayin sabon shugaban na PDP jihar Ekiti.
Sai dai TAM a cikin sanarwar bayan taro da ta fitar a Ado Ekiti, sun sanar da cewa mai gidansu Atiku da kuma kungiyar ba abin da ya shafe su wannan rikicin na cikin gida ne.
Ta yi kira ga shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, da ya shiga tsakani don a kawo karshen rikicin.