Abubakar Abba" />

ATM: Masu Ajiya A Bankunan Abuja Sun Koka Kan Yawan Cajin Da A Ke Yi Masu

Masu ajiyar kudaden su a bankuna a garin Abuja sun koka  akan cazar su da bankunan garin keyi sakamkon yin amfani da katin (ATM) don cire kudaden su.

Wasu daga cikin masu ajiyar kudaden sun shedawa kafar dillancin labarai ta kasa cewar, suna ganin tasku idan suka yi amfani da katin su na ATM don  fitar da kudi daga wasu bankunan da ba nan suke yin ajiya saboda cazar su naira 65 da ake yi ga dukkan hada-hada da suka yi.

A cewar wasu kwastomomi, mafi yawancin bankuna a garin, sun tsara injinan su na ATM don kawai injinan su dinga fitar da naira 10,000 kacal ko kasa da haka, inda a kai-kaice suke wanke abokan cinikayyar su da suke butar su fitar da kudi fiye da naira 10,000.

Abokan cinikayyan sunci gaba da kokawa akan cewar,in har suna son su fitar da naira 100,000 ko fiye da haka ta hanyar yin amfani da wasu bankunan ATM, don fitar da kudi daga wasu bankuna sun tabka asara sosai.

Sun yi kira ga babban bankin kasa (CBN) da sauran mahukuntan da abin ya shafa dasu kawo masu dauki don a taimakawa talakawa ‘yan Nijeriya masu ajiya a bankuna.

Wata mai suna Agatha Young, wadda take yin ajiya a First Bank ta ce, “Ina da zama a

anguwa Kubwa kuma dukkanin mashinan ATM dake yankin suna fitar da naira   10,000.

A cewarta,“a kwanan bays ina son in fitar da naiar 200,000 amma mashin din ATM na bankin da nake amfani dashi jama’a maso su fitar da kidi sunyi yawa, inda naje wani bankin don yin amfani da mashin din su na ATM, sai kawai na gano cewar,  mashin din ATM na bankin ya fitsr da naira 10,000 kawai ga dukkan ciniyar da kayi da bankin, inda naira 150,000 kawai na iya fitarwa saboda sauran mutane da suka zo fitar da kudi, suna kan layi suna jira kuma gashi na gaji da ci gaba da fitar da kudin ta hanya daya.

Ta kara da cewa,“na kuma gano cewar, an caje ni kimanin naira 1000 a wannan chinkiyar wanda wannan chajin ya yi yawan gaske.’’

Shi ma wani mai suna Sunday Mgbede, wanda yake yin ajiya a banki Gurantee Trust, mazauni a anguwar Nyanya a garin na Abuja yace, mafi yawancin mashinan ATM a unguwar su na fitar da naira 10,000 ne a dukkan nikayyar da kayi da bankunan.

Ya ce,“idan kana don ka fitar da kudi a cikin sati a wuraren Nyanya da Mararaba, zaka gano cewar mashinan ATM kadan suna fitar da sama da 10,000 ne kawai ga dukkan cinikayyar da ka yi.

Ya kara da cewar, “ya kamata hukumomin da abin dasu taimaka suyi dubi akan hakan domin jama’a suna jin jiki,domin babu kudi a kasar nan, kuma bankuna suna ta’azzara ma na saboda suna son su dinga yin arziki damu.”

Ya cigaba da cewa, “harda naira 65 da suke cazar mu da CBN ya bayar da umarnin a dinga cazar mu in anyi ciniyayya da bankuna har sau uku, ban jin cewar bankunan suna bin wannan ka’idar da CBN ya gindaya ta fitar da kudi.”

Har ila yau, itama wata mai yin ajiya a bankin First Bank mai suna Erica Jonah ta ce, ta yi amfani da katin ta ATM don fitar da naira 100,000 daga wani banki, inda ta gano cewar mashin din ATM na bankin an tsara shine yadda zai dinga fitar da naira 10,000 kawai ga dukkan chinikayyar da kayi da bankin kuma ana cajin naira 65 akan dukkan cinikayyar da ka yi da bankin.

Ta ci gaba da cewa, ba wannan ne karo na farko a gare ta ba, inda tace.wannan damfara ce kawai bankunan suke yi.

Ta yi kira ga mahunta a cikin harkar dasu yi dubi akan lamarin don a magance wannan damfarar da bankunan suke yiwa masu ajiyar kudaden su.

Bugu da kari, wata mai suna Gift Agbo, wadda tsohuwar ma’aikaciyar banki ce ta ce, mafi yawancin.mashinan  ATMs da bankuna suke amfani.dasu a kasar nan ba an tsara su bane daidai.da kudaden Nijeriya bane kuma hakan ne yasa bankunan suke fitar da kudi kadan.

Ta ci gaba da cewa,“wasu daga cikin mashinan na ATM, tsofaffi ne kuma ba’a tsara su akan irin kudin kasar nan ba.

Ta kara da cewa, takardun kudin da mafi yawancin bankuna suke zubawa a cikin  mashinan su na ATM, suma suna rage yawan kudin da mashinan ke fitarwa.

A cewarta,“bani da tabbacin cewar wannan matsalar za’a iya kawo karshen ta in har bankunan dake kasar nan suna zuba jarin su akan masu ajiya ta hanyar tsara mashinan su na ATM da suke samar da sauki ga a mazaunan mu.’’

A martanbin da sashen baiwa masu ajiya na CBN kariya ya yi yace, ya karbi korafi da dama daga gun masu ajiya a bankuna akan a sashen gabatar lamarin.

Babban manaja na sashen karbar korafi Fada Dabid ya baiwa masu ajiyar tabbacin cewar, CBN zai shawo kan lamarin.

A cewarsa,“kwarai mun karbi korafe-korafe akan cewar, misali in suka fitar da nair 40,000 daga wani banki kaza, duk da hakan basa sumun iya fitar da kudade da yawa idan su ka yi amgani da katin su ATM a wani bankin da ba a nan suke yin ajiya ba.

Ya ci gaba da cewa, “da farko dai ina son  dukkan alumar gari  su sani cewar, fitar da kudi ta hanyar mashin din ATM a ko wanne banki, ako wanne halin kaka bai kamata a caji mai ajiya ba har sai in ka fitar da kudi da ya wuce sau uku a cikin wata daya.

Ya kara da cewa,“idan kana yin amfani da katin ka na ATM, kana dadamar ka fitar da kudi mai ko sau nawa ne a cikin wata ba tare da

cazar ka komai ba.

Ya ce, ina son in kara wa masu yin ajiya kwarin gwaiwa suje bankunan da suke yin ajiya don su yi bincike akan wannan cajin da ake yi masu.

Mista Dabid ya kuma baiwa masu yin ajiyar dasu rungumi tsarin karancin zagayawar kudi da kuma yin amfabi wasu dabarun na biyan kudi kamar na POS da yin amfani da internet da sauran hanyar cinkayya ta wayar tafi da gidan ka don su rage dogaro akan gundarin kudi.

Ya yi nuni da cewar, “kana iya yin amfani da wasu hanyoyin na biyan kudi akan kaya da ayyuka, ya kara da cewar, zaka iya zuwa kasuwa don sayen wani abu ta hanyar gudanar da cinikayya da wayar ka tafi da gidan ka dake dauke da app, don ka biya kudin kayan da ka saya.

Dabid ya kara yin nuni da cewa, sai dai in har kana cikin matsananciyar bukatar kudi kana iya yin amfani da damar biyan kudi ta sauran hanyoyi.

Ya bayyana cewar, masu yin ajiyar suma suna da nauyi akan su inganta yadda bankunan da suke yin ajiya sunyi masu aikin da ya kamata ta hanyar rubutawa bankunan a hukumance akan rashin gamsuwa da yadda bankunan suke yi masu.

A karshe Dabid yace, ta haka ne kawai bankunan zasu shawo kan matsalar.

Exit mobile version