Daga Sulaiman Bala Idris, Abuja
A jiya al’umman Nijeriya, Arewa da ɗaukacin mutanen Jihar Jigawa suka tsinci kawunansu a cikin wani yanayi na jimami, sakamakon rasuwar Wazirin Dutse, AVM Mukhtar Muhammad.
Tun bayan da aka shelanta rasuwarsa, shugabanni da ɗaiɗaikun mutane suke ta nuna alhinin rashin shi ya kasance shugaba, uba, dan kishin ƙasa kuma dattijo wanda ya sadaukar da rayuwarsa kacokaf ga yi wa ƙasa hidima. Ya rasu yana da shekaru 73 a duniya.
Jami’i Ne Na Musamman -Shugaba Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a saƙon ta’aziyyar da yi ta marigayi AVM Mukhtar. Takardar wacce ta fito ta hannun mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu; Buhari ya misalta marigayin a matsayin jigo kuma mutum mai son ganin ci gaban Nijeriya.
Ya ce; “AVM Mukhtar mutum ne wanda yak e da aƙida da ƙa’idoji, waɗanda sune suka sa ya bar aikin soja ba tare da lokacin ritayansa yayi ba.
“Mutane ƙalilan ne a Nijeriya za su iya jure wa rasa aikinsu saboda aƙidarsu da ƙa’idarsu. Amma shi marigayi AVM Mukhtar ya aikata hakan, a daidai lokacin da masu riƙe da ofisoshin gwamnati suka fi muhimmanta mulkin da ƙa’idar tsarin rayuwarsu.” Inji shugaba Buhari
Shugaban ƙasan ya ƙara da nuni da irin rawar da marigayin ya taka wurin tabbatar da Jihar Jigawa a matsayin jiha. Sannan kuma ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga gwamnati, iyalai da al’umman jihohin Jigawa da Kano dangane da wannan babban rashi da aka yi. Ya kuma roƙi Allah ya kyautata makwancinsa.
Arewa Ta Yi Babban Rashi –Gwamnatin Jihar Jigawa
A saƙon ta’aziyyarsa, Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana rasuwar AVM Mukhtar a matsayin babban rashi ba kawai ga iyalansa, masarautar Dutse, da Jihar Jigawa ba, rashi ne ga Arewaci da ɗaukacin tarayyar Nijeriya.
Gwamnan ya ce, Marigayin ya yi rayuwa abin koyi, wanda ya kamata matasa su yi koyi das hi. Sannan daga ƙarshe ya roƙi Allah da ya gafarta masa kurakurensa, kuma Aljannah ta zama makomarsa.
Ɗan Ƙasa Ne Na Gari
–El-rufai
A sanarwar da gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar wacce kakakin gwamnan jihar, Samuel Aruwan ya rattaba wa hannu, gwamnan Jihar, Malam Nasir E-lrufai ya bayyana marigayin a matsayin ɗan ƙasa na gari. Gwamnan ya ce, “rasuwar marigayin ta kiɗima ni ƙwarai da gaske”.
El-rufai ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai son zaman lafiya wanda kuma ya kawo ci gaba a jihar lokacin da ya riƙe muƙamin gwamnan na Soja a jihar.
Ya ce, “A madadin gwamnatin Jihar Kaduna da kuma ɗaukacin al’ummar jihar muna yi wa iyalansa da abokansa ta’aziyya. Allah ya amshi uzurinsa. Aameen”
Tsayayyen Dattijo Ne
–Dattawan Arewa
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta bayyana cewa ta girgiza matuƙa tare da shiga wani hali da rasuwar mataimakin shugaban amintattu na ƙungiyar,AVM Mukhtar Mohammad (wazirin Dutse) wanda Allah ya amshi rayuwar a Birnin Landan shekaran jiya Lahadi.
A wata sanarwa wacce ta fito daga sakataren yaɗa labaran ƙungiyar, kuma aka rabawa manema labarai a garin Kadunƙa, ƙungiyar ta bayyana marigayi Mukhtar a matsayin wani tubali kuma tsayayyen dattijon da dattawan arewa ke alfahari da shi.
Daga ƙarshe, sanarwar ta bayyana cewa: “Ƙungiyar tuntuɓa ta dattawan arewa, tana miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalai, masarautar Dutse, gwamnati da al’umman jihohin Jigawa da Dutse dangane da rasuwar AVM Mukhtar Muhammad. Allah ya jiƙansa, ya kyautata makwancinsa. Allah kuma ya ba iyalansa haƙurin jure wa wannan babban rashi da muka yi gaba ɗayanmu.”
Ƙungiyar ta ce, a matsayin girmamawa ga wannan gwarzo, ta ɗage taronta na masu majalisar zartaswa wanda a baya ta shirya gudanarwa ranar Laraba mai zuwa 4 ga watan Oktoban 2017. Inda aka matsar da taron zuwa ranar 11 ga watan Oktoban 2017.