Maida hankali sosai yana da amfani saboda kuwa dole ne su tabbatar da cewar ana gudanar da ayyuka kamar yadda ya dace wato yadda doka ta ayyana ko ta tanadar.Jami’an ilimi akwai bukatar suna fahimta da ganewa kan al’amuran ilimin fasaha da yadda ake tafiyar da su.
Dole ne su yi kokari wajen koyon amfani da hanyoyi daban- daban nak afar sadarwa ta zamani saboda kuwa hakan zai taimakawa wajen bunkasa tafiyar da ayyukansu na jami’an ilimi ta hanyoyi da yawa.Daga karshe jami’an ilimi su tilastawa kansu son bunkasa ilimi da kuma ganin sai dalibai sun fara samun ci gaba kan sakamakon abinda suke koyo.Dole ne su kasance misali da karfafawa wasu da basu kwarin gwiwa su ma su kasance sai sun zama gwarzaye a vanagaren ilimi, duk da hakan kuma su kasance suna kokarin ganin sai an samar da tsare- tsare ko manufofi da za su taimakawa dalibai cimma nasara.
- Ayyukan Jami’an Ilimi Da Muhimmancinsu
- Hukumar Ilimin Bai Daya Za Ta Gina Dakunan Karatun Zamani A Makarantun Nijeriya
Kacokan, irin ilimin da ake bukatar jami’in / jami’an ilimi su kasance ya kasance sun san fannoni ko vangarori na ilimi,gogewa ko kwarewa, dabaru da kuma son lamarin aikin nasu har ga zuciya. Irin aiki ko gudunmawa da jami’an ilimi suke badawa bata wuce su tabbatar da cewa dalibai suna samun nagartaccen ingantaccen ilimi,su kuma hukumomin ilimi da al’umma su rika bada tasu gudunmawar bayan suma an taimaka masu domin a cimma muradan ci gaba da ingancin ilimi.
Ci Gaba Kan Ayyukan Jami’in Ilimi
Shi/su jami’an ilimi wadansu mutane ne da yakamata su da lamarin gudanar da ilimi har da tsare- tsare da manufofi a wata makaranta ko hukuma ana tafiyar da su kamar yadda ya dace. Hakanan ma ya dace su tabbatar da cewa cigaban tsarin manhajar koyarwa, koyon yadda ake koyarwa, irin sakamakon yadda dalibai suke koyo yana tafiya daidai da muradu, manufofin ita hukumar.Jami’an ilimi suna aiki da Malamai, masu tafiyar da lamarin ilimi,da sauran masu fada aji wajen samar da tsare- tsare da manufofi wadanda za su taimaka wajen bunkasa samuwar ingantaccen iulimi ga dalibai.daya daga cikin ayyukan jami’/ jamai’an ilimi shi ne na samar da aiwatar da tsare- tsaren ilimi, wadanda suke taimakawa muradan ko manufofin hukumar.
Wannan ya hada da yadda zai rika yin aiki yana tuntuvar Malamai da sauran kwararru ta fannin ilimi domin tabbatar muradan koyarwa, abubuwan ko daraussan da ake koyarwa, da yadda ake auna fahimtar daliban kan abinda aka koya masu, hakan ya yi daidai da abubuwan da su daliban suke son ko, ya kamata a koya masu da kuma ita hukumar makarantar.Hakanan ma jami’an iimin suna bibyar yadda ake aiwatar da tasare- tsare da manufofi,su kuma bada shawarwari yadda za a kara bunkasa lamarin, wannan kuma ya dogara ne kan irin bayanan da suka samu daga Malamai, dalibai, da sauran masu ruwa da tsaki .Akwai ma wani babban aikin jami’an ilimi wanda shi ne su bada dama yadda za a samu ci gaban Malamai, da sauaran kwararru ta vangaren ilimi.
Wannan ya kunshi shirya tarurrukan karawa juna ilimi,zuwa wasu muhimman taro, da horarwa lokaci zuwa lokaci wanda hakan zai sa a maida hankali ga sababbin hanyoyin koyarwa, bunkasa manhajojin da za a koyar, da irin dabarar da za ayi amfani da ita wajen lura da irin ci gaban da aka samu sanadiyar hakan.Jami’an ilimi suna bada tsarin koyarwa domin taimakawa Malamai wadanda watakila su kan fuskanci matsala wajen aikinsu na koyarwa, kamar yadda za su iya tafiyar da aji da kuma sa dalibai su kasance cikin koyarwar.Duk da hakan jami’an ilimi s uke da alhakin lura da yadda ko tsare- tsaren ilimin da manufofin sun dace da yadda ake so ko bukata.
Irin hakan ya hada da sanin yadda fahimtar ko kokarin daliban yake da kuma yin wani abu kan hakan, mai da hankalin Malami kan aikin shin a koyarwa, da sauran abubuwan da suke da alaka da samun nasarar ilimin da ake koyarwa. La’akari da hakan, suna iya bada shawarwari saboda a samar da sauye- sauye kan tsare tsare da manufofi, ko kuma su samar da sabbin hanyoyin da aka san ko tabbatar da za su bunkasa ganewar abinda ake koyawa dalibai wanda hakan zai sa a samu sakamakon da ake so. A takaice, ayyukan jami’in/jami’an ilimi suna da yawa sun kuma bambanta.Wadannan kwararrun suna bada muhimmiyar gudunmawa wajen tabbatar da cewa su tsare – tsare da manufofin ilimi suna tafiya kafada- kafada da bukatar dalibai da hukuma, su ma kwararrun fannonin ilimi suna samun irin gudunmawar da suke bukata domin su ma su zama suna gudanar da ayyukansu kamar yadda ya dace.