Bugu da kari jami’an ilimi suna iya suna lura da yadda za a tafiyar da kasafin kudin makaranta ko hukumar da ke da alaka da ilimi,samar da hanyoyin da suka dace da lamarin tallace- tallace,yadda za ‘a dauki Malamai, da ci gaba da tafiyar da lamura da su.
Idan ana bukatar samun nasara ta wannan bangare a matsayin sun a jami’an ilimi dole su kasance sun mallaki dabarun da za su taimaka ma su yin mu’amala, yin hulda,kai har ma da ganewa da fahimtar manufofin ilimi da yadda ake tafiyar da su.
- Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Gwaji A Kan Fasahar Sadarwa
- Sinawa Kimanin Miliyan 1.85 Za Su Rika Zuwa Yawon Bude Ido a Ketare Kullum Lokacin Hutun Bikin Bazara
Su san yadda za su lamarin da ya shafi aikinsu da masu fada aji/ruwa da tsaki,da suka hada da Iyaye, ‘yan makaranta/ dalibai, Malamai,da sauran kwararru.
Akwai kuma bukatar su rika yin tunani mai inganci,da kuma kirkirar abu, su kuma kasance suna tafiya daidai da zamani da yadda lamarin ilimin yake.
Gaba daya kacokam shi/su jami’in/ jami’an ilimi ayyukansu suna matukar wahala,sai dai akwai daukaka,lamarin da yake bukatar wanda/ wadanda suka amsa sunan sun mallaki yin tunani mai amfanarwa da wasu dabaru na nuna kauna ga lamarin daya shafi ilimi.
Ko suna aiki a makarantar Firamare ne ko, jami’a, jami’an ilimi suna bada muhimmiyar gudunmawa ta shata yadda al’umma za su iya kasancewa a gaba,da kuma tabbatar da cewa suna samun ilimi mai nagarta da taimaka masu domin cimma burinsu.
Dabarun Da Suka Kamata Jami’an Ilimi Su Mallaka
Sanin kowa ne jami’in ilimi kan shi ne alhakin tafiyar da al’amuran tsare- tsare da manufofin ilimi suka rataya kan shi, na makarantu da hukumomi.
Su ne wadanda ke a sahun gaba wajen lamarin da ya shafi ci gaban ilimi.
Ayyukan su suna da yawa shi yasa akwai bukatar su kasance sun mallaki/ko suna da dabarun da za su taimaka masu tafiyar da ayyukan su kamar yadda suka kamata.
Manyan dabarun da ake bukatar jami’in ilimi yana da su sun hada da babban lamari na yin mu’amala ta kud da kud da mutane, dabarar bincike da kuma nazari, yadda za a tafiyar da ayyuka,maganin matsalolin da za su iya tasowa, fahimta sosai tsare- tsare, da dokokin ilimi.
Yadda za ayi tuntuba ta sadarwa da masu ruwa da tsaki wadanda suke da yawa, da suka hada da Malamai, Iyaye, da kuma jami’an makarantu.
Ba ma kamar yadda za su tafiyar da manufofi da tsare- tsaren ilimi masu rikitarwa, su fahimci abubuwan da duk lamurran suka kunsa.
Jami’in ilimi akwai bukatar ace koda wane lokaci ya san halin da ake ciki na lamuran da suka shafi ilimi.Tafiyar da ayyukan ilimi wannan ma ana bukatar hakan ga jami’in ilimi ace ya san su,tsare-tsare da yadda za a aiwatar da su.
Hakanan ma akwai bukatar su tsara,shirya sosai,wajen aiwatar da yin ayyuka da tabbatar da kammala su cikin lokaci da kuma kudin da aka ware masu.
Dabarar da za ayi maganin matsaloli wannan ma ana sa ran jami’in ilimi ya mallaki hakan,su gano inda matsalolin suke da yadda za su yi maganin su manufofi da tsare- tsaren ilimi har ma da aiwatar da su,ana bukatar jami’in ilimi ya san da hakan.
Ana ma bukatar su ya zama sun sani sosai tsare- tsaren, dokokin ilimi karamar hukuma, Jiha, da kuma gwamnatin tarayya, wajen tabbatar da ana aiwatar da su kamar yadda dokoki suka tanadar kamar yadda ya dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp