Kimanin makarantun Firamaren gwamnati 19 ne wasu rahotanni suka nuna an rufe saboda yawaitar da hare-haren ‘yan bindiga kan wash al’ummomi a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.
Rufe makarantun ya shafi harkokin koyo da koyarwa na daliban da ba su gaza 9,113 da suka kunshi maza 4,819 da mata 4,294 da malamansu ba.
- Za Mu Ceto Duk Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Da Aka Sace – Irabor
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda, Sun Sace ‘Yan China 4 A Wajen Hakar Ma’adinai A Neja
Sakataren ilmi na jihar Katsina, Kabir Ali, wanda ya bayyana hakan, ya ce yawancin daliban makarantun da aka rufe sun koma garin Kankara domin ci gaba da karatunsu.
Ya koka da cewa lamarin ya haifar da cunkoson azuzuwa a hedikwatar majalisar, kuma yana yin illa ga ingancin ilimin da daliban ke samu.
Ya ce duk da kokarin da kungiyar UNICEF ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi, na daukar dalibai a makarantu, har yanzu akwai bukatar karin ajujuwa, malamai, da kayan koyarwa da kuma gyara gine-ginen da suka ruguje a makarantu.
Ya yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wajen gina karin ajujuwa domin daukar dalibai a yankin.
Hare-haren ‘yan bindiga na ci gaba da jefa rayuwar al’umma da dama bai a iya jihar Katsina ba, har sa jihohin Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Kaduna da kuma jihar Neja.