ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 27, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda, Sun Sace ‘Yan China 4 A Wajen Hakar Ma’adinai A Neja

by Sadiq
4 years ago
'Yan Bindiga

Akalla mutane 17 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani wajen hakar ma’adanai da ‘yan kasar China suke gudanarwa a Ajata-Aboki a unguwar Gurmana na karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Rahotannin sun ce an kai harin ne da yammacin ranar Laraba inda aka kashe mutane bakwai da suka hada da ‘yan sandan da ke gadin masu hakar ma’adinai da ma’aikata.

  • 2023: Bayan Buhari, Dole Dan Kudu Ya Zama Shugaban Kasa – Fayose
  • Wata Tawagar ‘Yan PDP Sun Koma APC A Jihar Osun

An ce maharan dauke da muggan makamai, sun isa unguwar ne da misalin karfe 2 na rana, inda suka nufi wajen da ake hakar ma’adinan, sannan suka bude wuta.

ADVERTISEMENT

Kwamishinan tsaron cikin gida da jin kai na jihar, Emmanuel Umar, ya tabbatar da faruwar harin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, sai dai ya ce kawo yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba.

Ya ce, “Gwamnatin Jihar Neja na son tabbatar da cewa a ranar 29/6/2022 da misalin karfe 2 na rana, bisa ga sanarwar da aka samu cewa ‘yan bindiga sun kai hari a wani wurin hakar ma’adinai da ke kauyen Ajata-Aboki ta gundumar Erena ta karamar hukumar Shiroro.

LABARAI MASU NASABA

NSCDC Ta Cafke Mutane 2 Da Ake Zargi Da Sace Kayan Titin Jirgin Kasa A Kano

Kuri’u Za Su Yi Tasiri A Zaɓen 2027, In Ji INEC

“An tura tawagar jami’an tsaro zuwa wurin domin kai dauki.”

Umar ya ce yayin da tawagar jami’an tsaro ta hadin gwiwa suka yi artabu da ‘yan bindigar, wanda ya yi sanadin asarar rayuka daga bangarorin biyu.

Ya kara da cewa, “Wani adadin ma’aikatan da ba a tantance ba a wurin hakar ma’adinan da suka hada da wasu ‘yan kasar China hudu an sace su.

“Jami’an tsaro sun hada karfi da karfe domin farautar sauran ‘yan bindigar tare da ceto wadanda suka jikkata ciki har da jami’an tsaro da suka samu raunuka daban-daban an kai su asibitin gwamnati da ke jihar domin yi musu magani.

“Yayin da gwamnatin jihar Neja ke jajantawa shugabannin hukumomin tsaro a jihar da kuma iyalan wadanda aka kashe, gwamnatin jihar ta ba da tabbacin cewa sadaukarwar da suka yi ba zai tafi a banza ba.”

Umar ya ce gwamnatin jihar ta amince da duk kokarin jami’an tsaro na hadin gwiwa da na al’ummomin jihar na ganin an shawo kan matsalar rashin tsaro a wasu sassan jihar.

Sai dai wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa “Kusan mutane 11 da suka hada da ‘yan sanda da mutane bakwai da ke aiki a wurin hakar ma’adinan da farar hula shida ne suka rasa rayukansu a harin.”

Ya ce an kai mutane da dama wadanda suka samu raunuka asibiti kuma suna cikin mawuyacin hali.

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Manyan Labarai

NSCDC Ta Cafke Mutane 2 Da Ake Zargi Da Sace Kayan Titin Jirgin Kasa A Kano

July 27, 2026
Rashin Tsaro Na Barazana Ga Zaben 2027 —Rahotanni
Manyan Labarai

Kuri’u Za Su Yi Tasiri A Zaɓen 2027, In Ji INEC

July 27, 2026
'Yan Bindiga
Manyan Labarai

Sojojin Ruwa Sun Cafke Jirgin Ruwa Maƙare Da Ɗanyen Mai Na Sata

July 26, 2026
Next Post
An Yanke Wa Dan Sandan Da Ya Kashe Direban Bas Hukuncin Kisa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Sufeton 'Yan Sanda A Ribas

LABARAI MASU NASABA

'Yan Bindiga

Tinubu Zai Ƙara Wa Sojoji Albashi Nan Ba Da Jimawa Ba – Ministan Tsaro

July 27, 2026
Har Kullum Sin Na Adawa Da Yadda Amurka Ke Siyasantar Da Batutuwan Fasaha Da Na Tattalin Arziki

Har Kullum Sin Na Adawa Da Yadda Amurka Ke Siyasantar Da Batutuwan Fasaha Da Na Tattalin Arziki

July 27, 2026
Kasar Sin Ta Gabatar Da Matsaya Game Da Matakan Karshe Na Bincike Mai Lamba 301 Kan Tilasta Yin Kwadago Da Amurka Ta Fitar

Kasar Sin Ta Gabatar Da Matsaya Game Da Matakan Karshe Na Bincike Mai Lamba 301 Kan Tilasta Yin Kwadago Da Amurka Ta Fitar

July 27, 2026
'Yan Bindiga

Taimakon Ƴan Bindiga: Kotu Ta Yanke Wa Mata 3 Hukuncin Shekaru 14 A Magarƙama

July 27, 2026
Sin Za Ta Ci Gaba Da Ingiza Kyakkyawan Yanayin Cinikayya Tsakaninta Da Nahiyar Afirka

Sin Za Ta Ci Gaba Da Ingiza Kyakkyawan Yanayin Cinikayya Tsakaninta Da Nahiyar Afirka

July 27, 2026
Sakamakon Dangantakar Sin Da Afrika Na Taba Mutane Masu Rauni Da Karamin Karfi

Sakamakon Dangantakar Sin Da Afrika Na Taba Mutane Masu Rauni Da Karamin Karfi

July 27, 2026
'Yan Bindiga

WAFU B 2026: Nijeriya Ta Doke Ghana Da Ci 4-2 A Wasan Farko

July 27, 2026
An Samu Karin Sabbin Abubuwa Da Sin Ke Fitar Wa Waje Da Ake Wa Lakabi Da “New New Three”

An Samu Karin Sabbin Abubuwa Da Sin Ke Fitar Wa Waje Da Ake Wa Lakabi Da “New New Three”

July 27, 2026
'Yan Bindiga

NSCDC Ta Cafke Mutane 2 Da Ake Zargi Da Sace Kayan Titin Jirgin Kasa A Kano

July 27, 2026
Saura Kwanaki 100 A Bude CIIE Karo Na 9

Saura Kwanaki 100 A Bude CIIE Karo Na 9

July 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.