Dan takarar shugaban kasa a karkashin lemar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, ya fito ya yi bayanin hakikanin abubuwan da suka wakana a tsakaninsu da jami’an hukumar kula da shige da fice a filin sauka da tashin jiragen na kasa da kasa da ke Heathrow a kasar Landan sa’ilin tafiyar da ya yi don bikin Ista.
A hirarsa da Arise News Channel ranar Talata da wakilinmu ya saurara, tsohon gwamnan Jihar Anambra ya fayyace abin da ya fahimta, inda ya ce, jami’an Gwamnatin Burtaniya ba su taba cafke shi balle su tsare shi ba.
Ya ce, abun da ya faru a filin Jirgin Heathrow, wani shigen binciken Immigration ne yayin da ya mika musu shaidarsa domin tantancewa sai suka yi zargin cewa an kwafi shaidarsa ko ironsa guda biyu ne don haka suka bibiyi bayanansa da gano cewa an kwafi irin nasa ne.
Obi ya ce, dan tsayar da shi na ‘yan mintina kawai aka yi sabanin bayanan da jam’iyyarsa ta fitar na cewa an dauki tsawon lokaci ana masa tukin tambayoyi.
Ya ce: “Sam kwata-kwata ba a kamani ba, ba a tsare ni ba. Sannan, ban aikata kowani irin laifi ba. An tsayar da ni a wurin binciken da aka saba na yau da kullum na hukumar kula da shige da fice saboda bayanan shaidata ya nuna shaida har biyu, kuma dududu bai wuce mintina 20 aka kammala komai.
“Ina rayuwa a Burtaniya tun 1993 har zuwa 2005. Daga wancan lokacin zuwa yanzu shekaru 30 kenan. Ba a taba zaunar da ni aka min tuhuma, kamawa ko tsarewa a kowace kasa a fadin duniyar nan. Ban tana samun kaina a bisa wani dalili da aka tuhumeni kan aikata wani laifi ba.
“A zahirin gaskiya, shigen binciken ne na yau da kullum, kuma jami’an sun bani dukkanin wata girmamawa sa’ilin da suke min tambayoyi, har ma suka shaida min cewa an kwafi shaidata don haka na kiyaye,” ya shaida.
Obi ya kara da cewa duk da yana da cikakken izirin zama a UK, amma ya zabi ya dawo Nijeriya, ya kara da cewa, “Ni haifafen dan Nijeriya ne. Ina kuma son na yi rayuwata a nan na mutu a nan gida Nijeriya”.
Ya ce, yana da rubutaccce bayani daga Gwamnatin Burtaniya da ke fayyace cewa ba tsare shi aka yi ba, illa iyaka an tsayar da shi a wurin binciken hukumar shige da fice domin duba bayanan shaidar shige da ficensa na ‘yan mintina kalilan.