A yau Litinin 13 ga wata, an gudanar da zaman tattaunawa karo na uku na majalisar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin, da kawancen majalisar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Afirka a nan birnin Beijing. Yayin taron, mahalarta fiye da 50 na kasar Sin da na kasashen waje sun yi musayar ra’ayi mai zurfi, bisa taken “gina shawarar ‘Ziri daya da hanya daya’ mai inganci, da hada kai wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a sabon zamani”.
A tsokacin sa, shugaban majalisar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin Zhang Qingli, ya bayyana cewa, ya kamata a himmatu wajen sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka, da karfafa musanyar fasahohi, da mai da hankali kan yin hakikanin hadin gwiwa, da aikata ra’ayin cudanyar bangarori da dama, kana da sa kaimi ga aiwatar da shawarar ci gaban kasa da kasa, da shawarar samar da tsaro a duniya, da shawarar raya wayewar kan duniya, da kuma tabbatar da nasarorin da aka cimma a dandalin tattaunawar hadin kan duniya, bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya” karo na uku, da nufin ba da gudummawar da ta dace wajen gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma. (Mai fassara: Bilkisu Xin)