Gwamnatin Jihar Katsina ta mayar da martani kan rahoton ƙungiyar agaji ta Medicins Sans Frontiers (MSF) wadda ta ce yara 652 sun rasu cikin watanni shida saboda ƙarancin abinci mai gina jiki.
MSF ta bayyana cewa a farkon watanni shida na bana, ta karɓi yara sama da dubu 70 a asibitocinta a Katsina, inda aka kwantar da kusan dubu 10, kuma 652 daga cikinsu sun rasu.
- Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi
- Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna
Ƙungiyar ta ce rage kuɗaɗen tallafin da ta ke samu daga ƙasashen waje na kawo cikas ga ayyukanta.
Amma gwamnatin Katsina, ta bakin shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko, Dokta Shamsuddeen Yahaya, ta ce duk da akwai yunwa, akwai kuma wasu cututtuka da rashin sani da ke haddasa mutuwar yara.
Ya ce shayar da yaro nonon uwa kaɗai a watanni shida na farko na hana kamuwa da wasu cututtuka, amma matsalar tsaro da wasu cututtuka na ƙara dagula lamarin.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙara kuɗi zuwa Naira miliyan 1,000 (wato miliyan 500 da aka ware a baya da ƙarin miliyan 500) domin magance matsalar yunwa a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp