Wasa tsakanin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Duniya wadda ake yiwa lakabi da Madrid Derby duba da cewa dukkan filayen ƙungiyoyin biyu ya na a babban birnin ƙasar Andalus wato birnin Madrid, ya tashi kunnen doki da ci 1-1.
An buga mintuna 45 na farkon wasan ba tare da wani ya jefa ƙwallo a raga ba, amma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ɗan wasan bayan Real Eder Militao ya jefa kwallo a ragar Athletico Madrid a minti na 65.
- Shin Barcelona Da Atletico Madrid Zu Su Iya Dakatar Da Real Madrid A La Liga?
- Yaushe Tauraruwar Mbappe Za Ta Fara Haskawa A Madrid?
Wasan ya samu tsaiko a minti na 70 bayan da wasu waɗanda ake hasashen magoya bayan ƙungiyar Athletico Madrid ne suka dinga yin jifa a cikin filin wanda hakan ya sa mai tsaron ragar Real Madrid Courtois ya janyo hankalin alƙalin wasa Mateo Bosquets inda shi kuma ya umarci ƴan wasa da su fice daga filin wasa kafin komai ya lafa.
Bayan an dawo ne a mintunan ƙarshe na wasan wanda aka yi ƙarin mintuna 20 sakamakon tsaikon da aka samu, Angel Correa ya jefa ƙwallo mai ƙayatarwa a minti na 95 kuma da haka aka tashi wasan.