Wasa tsakanin manyan ƙungiyoyin gasar Firimiya ta kasar Ingila Manchester City da Arsenal ya tashi babu ci a filin wasa na Etihad Stadium da ke Manchester.
Wasan wanda aka fara misalin karfe 4:30 na yammacin yau Asabar ya ɗauki hankalin masu sha’awar kallon kwallon kafa a fadin Duniya wanda hakan yasa gidajen sinima suka yi cikar kwari da magoya bayan kungiyoyin biyu.
- Gasar Firimiya: Arsenal Na Cikin Tsaka Mai Wuya
- Manchester United Na Fatan Tsawaita Kwantiragin Bruno Fernandez
Kamar kullum dai Erling Haaland ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal kafin sabon dab wasan Arsenal Caliafori ya farke a minti na 28,gab da za a tafi hutun rabin lokaci Gabriel Magalheas ya jefawa Arsenal kwallo ta biyu.
Duk da katin kora da aka baiwa Trossard a mintuna 45 na farkon wasan amma ta hana Manchester City kara kwallo cikin sauki,sai a mintunan karshe na wasan John Stones ya ci kwallon da ta mayar da City saman teburin gasar Firimiya.