Jami’in Huldada da jama’a na rundunar ‘yan sandan, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya ce babu wani dan Nijeriya da ke da hurumin tunkarar ‘yan sanda ko ramuwar gayya, ko da dan sandan ya mari wani farar hula.
Lokacin da Kakakin rundunar ke magana ta shafinsa na Tuwita, rundunar ‘yan sandan ta shawarci duk wani wanda aka yi wa zalunci da ya kai kara ga hukumar don tabbatar da doka da oda.
- ‘Yansanda Sun Yi Ruwan Tiyagas Kan Magoya Bayan Peter Obi A Ebonyi
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutane 5 Da Ake Zargi Da Hannu A Kisan Dan Sanata Gaya
Kakakin yana mayar da martani ne kan wani faifan bidiyo na wani mutum yana jan bindigu da wani dan sanda a lokacin da suka yi zazzafar cece-ku-ce da kuma cin zarafi ta wayar tarho.
Adejobi ya ci gaba da cewa, idan mutum ya afkawa jami’an ‘yan sanda sanye da kakinsu, za a yi masa kallon ya yi wa Nijeriya rashin mutunci.
Ya ce: “Ko dan sanda sanye da kakinsa ya mari farar hula, farar hula ba shi da ikon ramawa. Fiye da haka, idan yana sanye da kayan aiki, rashin mutunta Nijeriya ne ya doki jami’in da ke cikin kayan.
“Ba rashin mutuntawa ga dan sanda bane kadai, har al’ummarmu baki-daya kuma laifi ne kamar yadda dokokin mu suka tanada.
“Don haka, ba batun abin da dan sandan ya yi ne ya kai shi ba, sai dai martanin da farar hula ya yi wa ‘yan sandan a zahiri.
“Idan ‘yan sanda suka far wa farar hula, za ku kai rahoto kuma za a dauki mataki don tsawata masa, ba don daukar doka a hannunku ba.