ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kalaman John Kerry Sun Nuna Girman Kai Na Kasashen Yamma

by CMG Hausa
4 years ago
Kerry

Kalaman da manzon musamman na shugaban kasar Amurka mai kula da aikin tinkarar sauyawar yanayi John Kerry ya furta, a taron ministocin kasashen Afirka kan aikin kare muhalli, wanda ya gudana a kasar Senegal a kwanan baya, sun ba ni mamaki sosai.

Saboda a gaban wakilan dukkan kasashen Afirka, mista Kerry ya ce kasashe masu sukuni, ba su da wani nauyi na tarihi game da batun sauyawar yanayin duniya.

  • Buhari Zai Yi Balaguro Zuwa Kasar Amurka Gobe Lahadi

A ganinsa, aikace-aikace na daukacin dan Adam ne ke sa ake samun matsalar dumamar yanayi, saboda haka, ko da wata kasa dake fama da koma bayan tattalin arziki a nahiyar Afirka, wadda ke jin radadin bala’i daga Indallahi da sauyawar yanayin duniya ta haddasa, ya kamata ta dauki nauyi na tinkarar matsalar sauyawar yanayin da kan ta. Kana kasashe masu sukuni ba sa bukatar biyan diyya ga kasashen masu tasowa.

ADVERTISEMENT

To amma mene ne gaskiyar wannan batu? Sanin kowa ne, sannu a hankali, aikace-aikacen dan Adam na yin tasiri kan muhallin duiya. Tun kafin kasashe masu tasowa su fara raya masana’antunsu, kasashen yamma masu sukuni sun riga sun kwashe shekaru fiye da 200, suna kokarin bunkasa bangaren masana’antu, tare da fitar da dimbin iska mai dumama yanayi, da gurbata muhallin duniya sosai.

Hakan ya sa dukkan kasashe masu tasowa ke dauke da ra’ayin cewa, kamata ya yi, kasashe masu sukuni, da kasashe masu tasowa su dauki nauyi na bai daya, amma masu bambanci da juna, a yayin da ake tinkarar batun sauyawar yanayi.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Wannan ra’ayi ya nuna adalci, da dacewa da al’adar mutanen duniya, ta sanya wanda ya gurbata muhalli biyan diyya.
Sai dai maganar Kerry ta saba wa wannan ra’ayi na bai daya na daukacin kasashe masu tasowa.

Lamarin da ya sanya ‘yan Afirka fushi sosai: Wasu kungiyoyin jama’a da yawa na kasashe fiye da 40 dake nahiyar Afirka, sun nuna takaicinsu, inda suka ce John Kerry ya yi wasan fatar baki ne kawai, kana ya halarci taron ne don neman janyo hankalin mutanen duniya kan huldar dake tsakanin Amurka da kasashen Afirka.

Hakika, zancen Kerry ya nuna yadda kasar Amurka, da sauran kasashen yamma suke da girman kai.

A ganinsu, yadda kasashe masu tasowa suke tsayawa kan samun adalci, wani yunkuri ne na neman kudi kawai.
Ban da wannan kuma, Kerry ya yi gargadi ga kasashen Afirka, cewa kar su zuba kudi da yawa a aikin hakar iskar gas, duk da cewa akwai kasashen Afirka da yawa da suke kokarin raya bangaren iskar gas, don tabbatar da tsaron makamashi. A cewar John Kerry, ya kamata a raya makamashi da ake sabuntawa, maimakon iskar gas. Ya ce, “kar ku maimaita kurakuran da muka yi a baya.” Nufinsa shi ne, saboda kasashen yamma sun taba yin kurakurai, don haka a yanzu sun fi sanin hanya mai dacewa da ya kamata a bi ta.

Ya kamata kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa su bi umarnin kasashen yamma. A nan an nuna girman kai matuka.

Ta hanyar sauraron maganar John Kerry, za mu gane cewa, aikin tinkarar sauyawar yanayi ba shi da sauki. Kuma ba za a cimma nasara ba, sai dai in kasashen yamma daina nuna girman kai da son kai, sa’an nan su yi cudanya da kasashe masu tasowa cikin daidaito. (Bello Wang)

Kerry
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”
Daga Birnin Sin

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030
Daga Birnin Sin

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin
Daga Birnin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Next Post
Xi Da Takwaransa Na Togo Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Huldar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.