Bello, dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya ce, “bs laifi a binciki gwamnatin mahaifinsa, amma ya kamata a yi da zuciya daya ba don a wulakanta kowa ba ko neman mayar da martani biyo bayan wani sabani da ke tsakani.”
Bello mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa a majalisar dokokin kasa, ya bayyana haka ne a yayin da yake tattaunawa da BBC Hausa a ranar Lahadi, 9 ga watan Fabrairu, 2025.
- Gwamna Zulum Ya Mika Sandar Mulki Ga Sabon Shehun Dikwa
- Akwai Arzikin Duniya Da Na Lahira A Harkar Fim- Malam Inuwa
Ya kara da cewa, “ba aikinsa ba ne sasanta rikicin da ke tsakanin mahaifinsa da Uba Sani – gwamnan jihar Kaduna.
Abubuwan da ke faruwa a siyasar jihar a baya-bayan nan sun nuna cewa El-Rufai da Gwamna Sani suna takun saka. A watan Yunin 2024 ne Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta ba da shawarar a binciki El-Rufai kan zargin karkatar da kudaden al’umma.
Amma da yake magana a yayin tattaunawar, Bello ya ce, “Babu daya daga cikinsu (Sani da El-Rufai) da ya ba ni labarin rikicin; amma na fahimci cewa, komai ya wuce.”
Da aka tambaye shi ko zai iya sasanta mahaifinsa da Sani, Bello ya ce, “Ba aikina ba ne. Aikina shi ne in mayar da hankali wajen taimaka wa al’ummar mazabar Kaduna ta Arewa.”