Ƙungiyar shugabannin Matasa ta Nijeriya (CONYL) ta bayyana goyon bayanta ba tare da shakka ba ga Seyi Tinubu don ya shiga takarar zaɓen gwamnan Jihar Legas a 2027, inda ta bayyana cewa wannan dama ta kasance damarsa ta kundin tsarin mulki da kuma (amsa) “kiran allah.”
A cikin wata sanarwa da shugaban CONYL, Comrade Goodluck Ibem, ya sa hannu, ƙungiyar matasan ta musanta suka kan cancantar Seyi Tinubu saboda dangantakarsa da shugaban ƙasa Bola Tinubu.
- Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Shari’a Da Majalisa Su Yi Aiki Tare Kan Dokar Haraji
- Gwamnan Gombe Ya Aza Tubalin Gina Majalisar Dokoki Da Babbar Kotun Jiha Na Zamani
Ƙungiyar ta jaddada cewa Seyi Tinubu, a matsayin ɗan ƙasa Nijeriya, yana da hakkin yin zaɓe da kuma zama wanda za a zaɓa, ba tare da la’akari da iyayensa ba.
“Yawaitar kiran matasan Nijeriya na neman ya shiga takarar gwamnan Jihar Legas a 2027, kiran Allah ne mai nauyi wanda ba zai iya kauce masa ba,”.
Ƙungiyar ta tambayi me zai hana Seyi Tinubu, wanda aka bayyana a matsayin “mai kwazo, mai magana da hankali, da kuma basira,” ya sami damar yin aiki a gwamnati, musamman ma duba da kwarewarsa ta shugabanci.
CONYL ta kuma yi kira ga shugaban ƙasa Tinubu da ya ba da goyon bayansa ga burin ɗansa na zama gwamnan jihar, ta hanyar ƙa’idojin dimokuraɗiyya da kuma buƙatar al’ummar Legas.