Guda daga cikin dattawa a Masana’antar Kannywood, wanda ya daxe ana damawa da shi; tun daga shirin wasan dave, wasan kwaikwayo zuwa shirye-shiryen da ake aiwatarwa a halin yanzu; Kabiru Nakwango a wata tattaunawa da aka yi da shi ya bayyana cewa, fitowa da yake yi a matsayin malamin addini; a zahiri ba haka abin yake ba.
A hirar da Nakwangon ya yi da jaruma Hadiza Gabon, a cikin shirinta mai suna ‘Gabon’s Room Talk Show’; ya bayyana furodusoshin fim, a matsayin waxanda ke xora masa wannan nauyi na malanta; duba da cewa yana da ilimin addini bakin gwargwado da kuma xan fahimtar harshen larabci da ya yi.
- Ko Nawa Za A Bani Ba Zan Iya Fitowa A Matsayin Kwarto Ko Dan Daudu A Fim Ba -Dan Asabe Olala
- Ba A Kowane Irin Matsayi Zan Iya Fitowa A Cikin Shirin Fim Ba – Isa Bello Ja
Har ila yau kuma, ya bayyana rashin alaƙa ta kusa ko ta nesa da ƙasar Kwango; kamar yadda wasu ke tsammani, hasali ma bai tava ziyartar wannan ƙasa ba; illa kawai dai ya samu wannan suna ne a lokacin yarinta da wasu abokanai da sauran mutanen arziƙi ke kiran sa da shi, duk da cewa asalin sunan ba nasa ba ne.
Da yake amsa tambayoyi a kan yadda tarbiyar jaruman Kannywood, musamman mata a lokacin da da yanzu take, Nakwango ya yi nuni da cewa; abin ba a cewa komai, sakamakon yadda a halin yanzu abubuwan suka yi muni sosai; ta yadda wasu ke xaukar shigar banza a matsayin burgewa.
Daga Æ™arshe, ya bayar da shawara ga masu xaukar nauyin fina-finan Hausa a halin yanzu; da su tabbatar suna yin amfani da asalin halayya da al’adun Bahaushe, ba kawai su riÆ™a amfani da harshen Hausa suna aiwatar da abin da ko kaxan ba halayya ko al’adar Bahaushe ba ce