Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Jam’iyyar Adawa ta PDP a jihar Katsina ta ja hankalin ‘ya ‘yanta masu ta’ammuli da kafar sadarwa (Social Media) da su yiwa jam’iyya aiki da abubuwa na hankali ba wai cin fuska ga shugabanni ba kamar yadda wasu suka yi a baya.
Shugaban Jam’iyyar PDP a jihar Katsina Alhaji Salisu Yusuf Magijiri ya bayyana haka a wajen baddamar da shuwagabannin bananan hukumomi da za su ja ragamar tafiyar da harkar kafar zamani ta soshiyal midiya a jihar Katsina a barbashin jam’iyyar ta PDP.
Shugaban jam’iyyar ya ce PDP bata amince da cin zarafin wani ba ko wasu ba, saboda haka dole masu ta’ammuli da kafar sadarwa ta zamani a barbashin jam’iyyar PDP su bi tsarin jam’iyyar na girmama jama’a.
Haka kuma Alhaji Salisu Yusuf Magijiri ya zargin gwamnati mai ci yanzu da ciyo wa jihar Katsina bashi wanda ya ce a shekaru 16 da suka yi suna mulki ba su ciyo bashin ko kwabo ba.
Shi ma a nasa jawabin, baya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP wanda kuma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a zabe mai zuwa, wato Alhaji Umar Abdullahi da aka fi sani da TATA ya ja hankalin masu ta’ammuli da kafar sadarwa ta zamani wurin gudanar da ayyukansu.
Ya kuma bara da cewa akwai mutane da suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takara a nan gaba saboda haka kadda masu amfani da kafar sadarwa ta zamani a barbashin jam’iyyar PDP su haba masu neman takara faba.
Ya zuwa yanzu dai mutane hubu ne suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takara a zabe mai zuwa a barbashin inuwar jam’iyyar PDP wabanda kuma suke da magoya baya a kowane sabo da lungu na jihar Katsina, abin da ake jira a gani shi ne lokaci.