Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya ce, kasarsa ba ta da masaniya ko kuma hannu a kisan da aka yi wa Isma’il Haniyeh.
Sakataren harkokin wajen Amurkan, ya ce ba zai iya cewa ga abin da lamarin ke nufi ba, amma ya jaddada muhimmancin samun tsagaita wuta a Gaza.
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa Kan “Kara Zurfafa Gyare-gyare A Sin Dama Ce Ga Duniya” Da Kuma Musayar Jama’a Tsakanin Sin Da Masar Na Shekarar Hadin Gwiwa
- Kano Pillars Ta Raba Gari Da Kocinta, Paul Offor
Shi kuwa Firaiministan Qatar, wadda ke shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wutar da ake yi, ya ce mutuwar Haniyeh za ta iya kawo cikas a tattaunawar da ake yi.
Rasha da China da kuma Turkiyya duk sun yi Allah-wadai da kisan da aka yi masa, inda shugaba Erdogan ya ce an yi hakan ne da nufin karya lagon Falasdinawa.
Wata mata a Tehran ta ce akwai bukatar mu yi Allah-wadai da wannan ta’addanci da aka yi, sannan ina so Isra’ila ta sani cewa al’ummar mabiya shi’ar Iran ba za su taba bari a kashe musu bako a kasar kuma su yi shiru ba.