Daga A.A.Masagala, Benin
A wata hira da LEADERSHIP A YAU ta yi kwanan nan tare da jagoran Fulani Makiyaya mazauna yankin Kudu maso-gabas a Kudancin kasar nan, Malam Ardo Sa’idu Baso, Ardon ya bayyana cewa shi da jama’arsa suna zaune kalau da abokan zamansu a yankin.
Jagoran y ace, “Babu shakka muna da kyakkyawar alakar zamantakewa tsakanin mu Fulani makiyaya da kuma ’yan kabilar Ibo. Duk da cewa wannan matsala ta kungiyar Biyafara ta faru amma mu a nan Jihar Enugu tashin hankalin bai shafe mu ba, sai dai irin abin da ba a rasawa”.
Ya ci gaba da cewa, “Kafin irin wannan mastalar ta fara tasowa da bayan faruwarta zan iya cewa akwai zaman lafiya awannan jihar sama da shekaru talatin da muke tare da su.
Kazalika, jagoran Fulanin ya ce a duk lokacin da suka ga wani ya taso wanda ka iya haifar da rashin jituwa a tsakani, sukan nemi abokan zamansu ne su zauna tare su yi tattauanawa ta fahimtar juna domin samun mafita ko maslaha. Idan darna ce da dabbobi suka yi, sai a yi wa barnar kima su biya mai gona hakkinsa.
A karshe, Ardon ya yi kira ga takwarorinsa a duk inda suke da su tashi tsaye su tabbatar da adalci tare da kare hakkokin jama’arsu. Sannan su yi dukkan mai yiwuwa wajen wanzan da zaman lafiya a tsakani.