• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Mu Iya “Gina” Ayaba A Amurka

by CGTN Hausa and Sulaiman
2 months ago
in Ra'ayi Riga
0
Ba Mu Iya “Gina” Ayaba A Amurka
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

MADELEINE DEAN: “Ayaba, yanzu harajin nawa ne a kanta? Amurkawa na son ayaba, biliyoyin ayaba muke ci a kowace shekara.”

HOWARD LUTNICK: “Ya danganta da kasar da ta samar da ita, yawanci kaso 10% ne.”

MADELEINE DEAN: “Haka ne, kaso 10%, kuma tuni Walmart ya daga farashin ayaba da kaso 8%.”

HOWARD LUTNICK: “Ba za mu sanya haraji a kan abin da aka gina ko kayayyakin da aka samar a Amurka ba, wannan tabbas ne.” (There’s no uncertainty: if you build in America and you produce your product in America, there will be no tariff.)

MADELEINE DEAN: “Amma ba za mu iya ‘gina’ ayaba a Amurka ba”. (We can’t build bananas in American.)

Labarai Masu Nasaba

Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!

Tursasawa Kasashen Afirka Karbar Bakin Haure Daga Amerika Kuskure Ne

A wani taron sauraron bayanai da aka gudanar a kwanan baya, ‘yar majalisar wakilan kasar Amurka Madeleine Dean ta yi wa ministan kasuwanci na kasar, Howard Lutnick tambayoyi game da yanayin ciniki da manufofin harajin kwastam na kasar, inda ta tono shirmen da ke cikin matakan haraji da Amurka ta dauka a kan kayayyakin da take shigarwa daga kasa da kasa. Kasancewar ayaba tana girma ne a sassa masu zafi, galibin yankunan kasar Amurka ba su dace da nomansu ba. Ko a jihohin Hawaii da Florida da sauran sassan kasar Amurka da suka fi zafi ma, yawan ayabar da ake samarwa ba zai iya biyan bukatun kasuwannin Amurka ba, sabo da wasu dalilai na yanayi da kasuwanci.

A hakika, a yayin da tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen duniya ke kara dunkulewa baki daya, kasa da kasa su kan samu mabambantan fifiko a sana’o’i daban daban sakamakon bambancin albarkatun da suke da su, ko kuma bambancin ci gabansu, lamarin da ya sa suke yin musayar kayayyakin da suke da fifikonsu don tabbatar da bunkasa ta bai daya, hakan nan kuma sana’o’i daban daban na dogara ga juna. Kamar yadda sauran kasashen duniya suke, kasar Amurka ita kanta ta amfana da bunkasuwar tattalin arzikin duniya da kuma ciniki mai ‘yanci.

Duk da haka, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauki matakan haraji na barkatai a yunkurin daidaita matsalar da ya kira wai “gibin kudin ciniki”, matakin da ba haifar da munanan matsalolin haraji a fadin duniya kawai ya yi ba, har da daga farashin kayayyaki a cikin kasar kansa. Lallai Amurka tana fama da rashin lafiya, amma ta sa sauran kasashe shan magani. Hakan ba zai taimaka ga daidaita matsalolin da tsarin tattalin arzikin kasar ke haifarwa ba, sai ma kara tsunduma shi cikin mawuyacin yanayin tattalin arziki. (Mai Zane:Mustapha Bulama)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sarki Sanusi II Ya Yi Hawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda Na Haramta Hawan Sallah A Kano

Next Post

Mutum 10 Sun Mutu Sakamakon Harbe-harbe A Makarantar Sakandire A Kasar Austriya

Related

Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!
Ra'ayi Riga

Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!

3 days ago
Tursasawa Kasashen Afirka Karbar Bakin Haure Daga Amerika Kuskure Ne
Ra'ayi Riga

Tursasawa Kasashen Afirka Karbar Bakin Haure Daga Amerika Kuskure Ne

3 days ago
Wace Kasa Ce Take Son Zama “Kasa Ta Uku Mai Tsaro” A Wurin Amurka?
Ra'ayi Riga

Wace Kasa Ce Take Son Zama “Kasa Ta Uku Mai Tsaro” A Wurin Amurka?

1 week ago
Lai Ching-Te Bai Cancanci Zama Jagoran Yankin Taiwan Ba
Ra'ayi Riga

Lai Ching-Te Bai Cancanci Zama Jagoran Yankin Taiwan Ba

1 week ago
Manufar Raya Biranen Kasar Sin: Ba Wai Kawai a Tabbatar Da “Tsayi” Ba Ne Har Ma Da “Zafi”
Ra'ayi Riga

Manufar Raya Biranen Kasar Sin: Ba Wai Kawai a Tabbatar Da “Tsayi” Ba Ne Har Ma Da “Zafi”

1 week ago
Girman Kai Da Son Zuciya Ba Za Su Sa A Amince Ko Ba Da Hadin Kai Ba
Ra'ayi Riga

Girman Kai Da Son Zuciya Ba Za Su Sa A Amince Ko Ba Da Hadin Kai Ba

2 weeks ago
Next Post
Mutum 10 Sun Mutu Sakamakon Harbe-harbe A Makarantar Sakandire A Kasar Austriya

Mutum 10 Sun Mutu Sakamakon Harbe-harbe A Makarantar Sakandire A Kasar Austriya

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

July 26, 2025
Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

July 26, 2025
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

July 26, 2025
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

July 26, 2025
Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

July 26, 2025
Amurka

Natijojin Auren Dattijo Ga Budurwa

July 26, 2025
An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu

An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu

July 26, 2025
Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (6)

Dalilan Da Suka Sa Cinikin Bayi Bai Yi Nasara A Arewacin Nijeriya Ba

July 26, 2025
Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko

Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko

July 26, 2025
Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

July 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.